--
NAPTIP ta kama masu safarar mutane 86 a Kano, ta ceto mutane 135

NAPTIP ta kama masu safarar mutane 86 a Kano, ta ceto mutane 135

Hukumar, Yaƙi da masu safarar mutane, NAPTIP ta ce taceto mutane 135 daga watan Janairu zuwa Satumban 2020 a Kano

Hukumar ta kuma ce ta yi nasarar kama mutum 86 da ake zargi da safarar mutanen; 44 mata, 42 maza

NAPTIP ta gargadi yan Najeriya masu niyyar zuwa ƙasashen waje ci rani su rika yin takatsantsan da ƴan damfara Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane na Ƙasa,

NAPTIP ta ce ta ceto mutane 135 tare da kama mutum 86 da ake zargin masu safarar mutane ne a Kano daga watan Janairu zuwa yanzu.

Kwamandan hukumar a jihar Kano, Shehu Umar ne ya bayyana hakan yayin hirar da Kamfanin dillancin labarai, NAN, ta yi da shi ranar Talata a Kano.

Ya ce mutane 135 da aka ceto sun kunshi mata 112 da maza 23. Mista Umar ya cigaba da bayanin cewa rundunar ta samu rahoton wadanda ake zargin da laifuka kamar fyaɗe, azabtar da yara, safarar yara da sauran su.

Kwamandan ya ce an mika 21 cikin wadanda aka kama zuwa ga hukumomin da ya dace su bincike su.

Kazalika, ya ce cikin wadanda ake zargi 86 da aka kama 44 mata ne yayin da 42 maza ne.

"Bayan samun bayanai, hukumar ta yi bincike daga watan Janairu zuwa Satumba inda ta yi nasarar kama wadanda ake zargi da ceto mutane," in ji shi.

Ya ce a halin yanzu hukumar ta shigar da kararraki 9 a kotu kuma za ta shigar da wasu sabbin 10. Kwamandan ya gargadi yan Najeriya a kan tafiye-tafiye zuwa kasashen waje domin neman arziki ba tare da sun yi sahihin bincike ba.

Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


0 Response to "NAPTIP ta kama masu safarar mutane 86 a Kano, ta ceto mutane 135 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?