LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Fasinja 1 ta ji rauni a harin da aka kaiwa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna


Hukumar yan sanda ta yi tsokaci kan harin da aka kaiwa jirgin Abuja zuwa Kaduna ranar Litinin - Hukumar ta karyata rahoton cewa yan bindiga ne suka budewa jirgin wuta 

An tabbatar da akalla Fasinja daya ta ji rauni sakamakon harin Hukumar yan sandan Najeriya ta saki jawabi akan harin da aka kai wa fasinjojin jirgin kasa tsakanin garin Rijana da Garin dake hanyar Abuja zuwa Kaduna a daren Litinin. 

Kakakin hukumar na jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya bayyanawa kamfanin dillancin labarai NAN a hirar wayar tarho cewa jirgin ya isa Kaduna lafiya. Ya tabbatar da labarin cewa wasu matasa ne suka jefi jirgin da duwatsu a kauyen Rijana, cikin Kaduna. 

"Ba harsashi bane ko kwari da gwafa, abinda suka yi jifa da shi ba mugun makami bane. Ba wani hari bane, jirgi na tafiya. Jami'anmu dake Rijana na kan lamarin," Ya ce 

"Kawo yanzu babu wanda aka kama amma mun tura jami'an wajen domin damke masu jifan," 

Amma yan sanda sun ki bayyana cewa wata fasinja a jirgin ta samu rauni sakamakon harin. Premium Times ta samu labarin cewa matasan sun kai hari ne misalin karfe 7:30 yayinda jirgin ya nufi Kaduna. Jifan da sukayi wanda ya fasa gilashin jirgin ya samu wata mata kuma ta ji rauni. 

Domin gudun masu garkuwa da mutane da suka addabi hanyar Abuja zuwa Kaduna, matafiya sun koma hawa jirgin kasa saboda ya fi tsaro da kwanciyar hankali. Amma da yiwuwan mutane su fara tsoron jirgin saboda hare-hare irin wannan. Da alamun masu garkuwa da mutane sun koma babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna inda suka addabi matafiya a watanni baya kafin jami'an tsaro suka damke da dama cikinsu. A ranar Juma'a, 4 ga Satumba, wasu fasinjoji sun tsallake rijiya da baya yayinda Sojoji suka kai musu dauki ana gab da awon gaba da su. 

Legit ta samu yadda jami'an Soji da yan sanda suka fitittiki masu garkuwa da mutanen cikin daji kuma dukkan fasinjojin da akayi kokarin sacewa suka samu rauni. A jawabin da kwamishanan tsaron jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya saki ya bayyana yadda jami'ai ke farautar yan bindigan. 


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


Post a comment

0 Comments