LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

‘Najeriya Ta Kusa Durkushewa A Hannun Buhari’- Sugabannin Kungiyoyi


Shugabannin manyan kungiyoyi biyar na yankunan Najeriya sun ce “Najeriya na gab da kaiwa gargara” kamar yadda Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya fada.

A taronsu na kwana biyu ne Obasanjo ya caccaki Shugaba Buhari kan gazawar gwamnatinsa da kuma karuwar rarrabuwar kan ‘yan Najeriya.

Mahalarta taron sun goyin bayan Obasanjo da cewa martanin Fadar Shugagaban Kasa ga kalaman tsohon shugban yarinta ce kuma “babban abin takaici da damuwa”.

Kungiyoyin da sun hada da ta Yarbawa zalla, Afenifere; Kungiyar Dattawan Arewa (NEF); Ohanezen Ndigbo ta ‘yan kabilar Ibo; Kungiyar Yankin Neja Delta (PANDEF); da kuma ta Yankin Middle Belt (MBF).

Sun bayyana fushinsu ce Fadar Shugaban Kasa na neman nuna kamar ba ta san da taron da Obasanjo ya kira ba na tattaunawa tare da bayar da shawarwarin magance matsalolin da ke barazana ga hadin kan kasar.

Aminiya ba ta kai ga samun jin ta bakin Fadar Shugaban Kasa game da matsayin kungiyoyin ba, amma wani wani jami’in gwamnati ya ce babu bukatar musayar yawu da kungiyoyin a kan batun.

Wata majiya da ke da kusanci da abin da ya wakana a taron kungiyoyin kabilun da Obasanjo ta ce gwamnoni uku masu ci sun halarci zaman, ciki har da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya (NGF), Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti, sai kuma Atiku  Bagudu na Jihar Kebbi da kuma Aminu Waziri Tambuwal na Jihar Sakkwato.

“Wannan alama ce ta kyawu da sahihancin manufarmu. Duk da bambance-bambancenmu, mutane daga jam’iyyu daban-daban sun halarci taron kuma abun da ake bukata shi ne gwamnati ta kalli sakon ba mai sakon ba”.

Sanarwar da Kakakin Afenifere, Yinka Odumakin ya fitar a madadin kungiyoyin ta yi mamaki cewa “kyakkyawar manufa da yunkurin kwantar da hankali da dawo da kyakkayawar fatar hadin kai da dorewar kasarmu zai sa Fadar Shugaban Kasa ta caccake mu har ta ce mana ‘yan ta’adda”.

Masu magana da yawun kungiyoyin sun hada da Dokta Hakeem Baba-Ahmed, Cif Guy Ikokwu, Sanata Bassey Henshaw da kuma Dokta Isuwa Dogo. Sun yi gargadin cewa halin da ake ciki barazana ce ga dorewar kasar.

Suka ci gaba da cewa “ba ma nadamar taruwa da musayar fahimta da kuma sadaukar da kawunanmu domin ceto kasarmu daga durkushewa.

“Yadda Fadar Shugaban Kasa ta mayar da martani ga wannan yunkuri namu da wani tsohon shugaban kasa, abin takaici ne”.

“Akwai damuwa yadda Fadar Shugaban Kasa ke yin halin ko-in-kula wanda hakan ke sun sanyayar masu yunkuri da kshin kasawajen magance matsaoli ta yadda take rikon al’aumura tsaro da cigaban kasa da kuma tattalin arziki”, inji taron.

Sun bayyana kwarin gwiwarsu na ci gaba da bin hanyoyi masu tasiri wurin tattaunawa domin tabbatar da dorewa da kuma dunkulewar Najeriya cikin adalci.

“Za mu ci gaba da amfani da ‘yancinmu na tattaunawa da neman mafita tare da sauke nauyin da ke kanmu na ‘yan Najeriya masu tasowa da suka cancanci rayuwa a kasar ba tare da sun fuskanci wani tasgaro ba.

“Mun yi amannar cewa ya kamata Fadar Shugaban Kasa da ‘Yan Majalisa da ‘yan Najeriya na gari su ba wa wanna shiri hadin kai.

“Idan Fadar Shugaban Kasa ta kaurace masa, to ‘yan Najeriya na da damar tambayar ta me take yi domin magance matsalolin da suka yi  wa kasar kakagida.

“Ya kamata Shugaba Muhammadu Buhari ya sani cewa ‘yan Najeriya za su iya bambance tsakanin wadanda suka damu su yi wani abu da kuma masu iko da suka ki yin komai”, inji sanarwar.


Source: Aminiya Daily Trust


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


Post a comment

0 Comments