LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Mutum 4 ƴan gida ɗaya sun mutu a hatsarin mota a Jigawa

Mutane huɗu ƴan gida ɗaya sun mutu a wani mummunan hatsarin mota da ya faru a hanyan Kano zuwa Jigawa a ranar Asabar.

Wani ɗan uwan wadanda suka rasu, Shehu Yusuf Kazaure ya ce dukkan wadanda suka mutu ƴan gidan Hajiya Safiya Mohammed ce, direktan Ilimin gaba da sakandare a ma'aikatar Ilimi na jihar.

Suna kan hanyarsu ta zuwa ƙaramar hukumar Malam Madori ne ɗaurin aure yayin da motarsu ta yi Kundin bala a kusa da Danladin-Gumel a ƙaramar hukumar Gumel.

"Hadarin ya faru ne a yammacin ranar Asabar. "Uku cikin yaran Hajiya Safiya; Fati, Abba da Zainab sun mutu nan take.

"An tafi da su Malam Madori. Amma ko da suka isa can, Hanan, ɗiyar Zainab ita ma ta cika. "Abin baƙin ciki ne ga iyalan domin yawancin mu mun zubar da hawaye.

"Mutuwar mutum huɗu ƴan gida ɗaya a rana guda ba ƙaramin lamari bane. "Lallai abin baƙin ciki ne, ina addu'ar Allah ya gafarta musu," in ji Kazaure. Ya ce an yi musu jana'iza a Malam Madori bisa koyarwar addinin musulunci.


Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


Post a comment

0 Comments