LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Idan kana tsoron mutuwa a shekaru 70, to ka binciki imaninka - Malamin coci


Fasto Adeboye ya yi addu’a kan korona a yayin addu’ar Lahadin farko na cocin RCCG - Malamin ya ce Allah ya adana mutanensa har watan Satumba sannan zai kare su daga cutar 


An bukaci jama’an taron da su ci gaba da gode ma Allah kan ayyukan ban sha’awa nasa Shugaban cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG), Fasto Enoch Adeboye ya ce duk mutumin da ya fi shekaru 70 kuma yake tsoron mutuwa akwai bukatar ya binciki imaninsa. D


a yake wa’azi a lokacin taron godiya na sabuwar shekarar RCCG wanda aka gudanar a hedkwatarta da ke Lagas, malamin ya bayyana cewa shawarar da gwamnati ta bayar na hana tsoffi zuwa coci abu ne mai kyau. Sai dai Adeboye, ya yi wata tunatarwa a kan mutuwa, cewa sakon Ubangiji zai isa a kan duk wani mai rai, NAN ya ruwaito. 

“Saboda annobar Coronavirus, an shawarci tsoffi da su zauna a gida sannan kada su zo coci wanda hakan shawara ce mai kyau. “Amma idan ka fi shekaru 70 sannan kuma kana tsoron mutuwa, toh lallai ka binciki imaninka,” in ji malamin. 


Shugaban na RCCG ya bayyana cewa Allah zai halaka coronavirus kuma babu annobar da za ta kusanci ‘ya’yansa. “Allah zai bamu cikakken nasara a kan kowace cuta. Allan da ya barmu har muka ga watan Satumba zai barmu mu ga sabuwar shekara,” ya yi addu’a.

 Malamin ya bukaci taron jama’an da kada su daina yi wa Allah godiya a kan dukkanin abubuwan da Ya yi. A ranar Talata, 25 ga watan Agusta, RCCG ta sanar da cewa za ta gudanar da taro a watan Satumban 2020 ta yanar gizo. 

A cewar cocin, za ta ci gaba da tsarinta na gudanar da tarukan addu’a ta yanar gizo. Legit.ng ta rahoto cewa a wata sanarwa daga mahukuntan sun ce Fasto Adeboye ne ya yanke hukuncin domin kada ya jefa kowa cikin hatsari idan suka fito daga gidajensu don halartan taro. 


Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments