--
Buhari zai shilla kasar Nijar yau litinin

Buhari zai shilla kasar Nijar yau litinin


Shugaba Muhammadu Buhari zai shilla kasar Nijar ranar Litinin domin halartan taron shugabannin kasan yankin Afrika ta yamma karkashin gammayar ECOWAS. Mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan ranar Lahadi, a shafinsa na Tuwita. 

Ya ce Buhari zai samu rakiyar manyan ministocinsa kuma zai dawo bayan zaman. Garba Shehu yace: "Shugaba Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa Niamey, jamhurriyar Nijar domin halartan taron gangamin shugabannin kasar yankin Afrika ta yamma ECOWAS karo na 57. 

"A taron da za'ayi cikin kwana daya, za'a tattauna kan rahoto na musamman kan COVID-19 da shugaba Buhari zai gabatar bayan nadashi zakaran yaki da COVID-19 a taron yanar gizon da akayi ranar 23 ga afrilu, 2020." 

"Hakazalika za'a tattauna kan lamarin ta'addanci, barandanci da kuma juyin mulkin da Sojoji sukayi a kasar Mali." 

"Bayan haka, za'a tattauna kan zabukan yan majalisa da shugaban kasa da zasu gudana shekaran nan a Burkina Faso, Cote d'ivoire, Ghana da Nijar." 

Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Buhari zai shilla kasar Nijar yau litinin"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?