--
Duba Jerin mutum 9 a Kano da aka yankewa hukuncin kisa a 2020

Duba Jerin mutum 9 a Kano da aka yankewa hukuncin kisa a 2020

Bayanai sun nuna cewa a kalla mutum tara aka yanke wa hukuncin kisa a jihar Kano da ke yankin arewacin Najeriya daga farkon shekarar 2020 zuwa watan Augusta.

Kamar yadda takardun kotu daban-daban suka bayyana kuma BBC ta gani, an yanke wa mutanen hukuncin kisan bayan samunsu da aka yi da wasu manyan laifuka.

Bakwai daga cikinsu sun samu hukuncin kisan bayan da aka kama su da laifin kisan kai, daya daga ciki ya yi wa karamar yarinya fyade sai guda daya da yayi batanci ga Annabi Muhammadu (SAW).

Idan za mu tuna, Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya dauka alkawarin saka hannu a kan takardar kashe Yahaya Sharif-Aminu, matashin da aka kama da laifin batanci ga Annabi.

Ga jerin mutanen da aka yanke wa hukuncin kisa a jihar Kano daga watan Janairun shekarar nan zuwa watan Augusta.

1. Ali Abdullahi: A ranar 11 ga watan Fabrairun da ta gabata, wata kotu a jihar Kano ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.


2. Yakubu Dalha: Wata kotu mai lamba shida a birnin Kano ta yanke masa hukuncin kisa sakamakon kama shi da tayi da laifin kisan kai a ranar 3 ga watan Maris na wannan shekarar,


3. Abdullahi Isyaku: Babbar kotu a jihar Kano ta kama shi da laifin kisan kai, lamarin da yasa ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 16 ga watan Maris.

4. Mujahid Sa'id: Wata kotu mai lamba 13 ta kama Mujahid da laifin kisan kai a ranar 24 ga watan Maris. Hakan yasa aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

5. Naziru Ya'u: An yanke wa Naziru Ya'u hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 26 ga watan Yuni bayan kama shi da aka yi da laifin kisan kai.


6. Shehu Ado Shehu: Wata kotu mai lamba 6 ta yankewa Shehu Ado hukuncin kisa ta hanyar rataya a ranar 26 ga watan Yuni bayan kama shi da tayi da laifn kisan kai.


7. Isah Auta: An yanke wa Auta hukuncin kisa a ranar 29 ga watan Yunin 2020, bayan kama shi da aka yi da laifin kisa. Za a kasheshi ta hanyar rataya.


8. Yahaya Aminu: babbar kotun shari'ar Musulunci da ke Kano ta kama Yahaya Aminu da laifin batanci ga Annabi Muhammadu. A ranar 10 ga watan Augustan 2020, kotun ta yanke wa matashin mawakin hukunci kisa ta hanyar rataya.


9. Mati Abdu: Babbar kotun shari'ar Musulunci da ke birnin Dabo ce ta kama tsohon da laifin fyade. Ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar jefewa a ranar 12 ga watan 12 ga watan Augusta.

Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Duba Jerin mutum 9 a Kano da aka yankewa hukuncin kisa a 2020 "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?