LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Messi ya koma bakin aiki yana atisaye a baselona

Messi, mai shekara 33 a duniya, ya mikawa Barcelona takardar cewa yana son tafiya ranar 25 ga watan Agustan daya gabata sai dai ranar Juma’ar da ta wuce ya bayyana cewa zai ci gaba da zama a Barcelona, sakamakon ba zai yiwu wata kungiya ta iya biyan farashin da kungiyarsa take nema a kansa ba.

Wannan ne karon farko da dan kasar ta Argentina ya yi atisaye tare da abokansa da ke kungiyar tun bayan zuwan sabon mai koyarwa Ronald Koeman, wanda aka bayyana cewa Messi baya farin ciki da zuwansa kungiyar.

Barcelona za ta yi wasanta na farko a gasar  La Liga ta bana ranar 27 ga watan Satumba inda za ta fafata da Billarreal wasan dai ake ganin dan wasan zai fara fafatawa sai dai babu tabbas idan zai buga wasannin sada zumuntar da kungiyar zata fafata a ‘yan kwanakin nan.


Messi bai halarci gwajin cutar korona da kungiyar ta yi wa ‘yan wasanta ranar 30 ga watan Agusta ba kuma bai yi atisaye ba tun bayan da ya aike wa kungiyar takardar son barinta sai dai yanzu ana ganin zuciyar dan wasan tayi sanyi.

Barcelona da La Liga sun dage cewa ba zai bar kungiyar ba sai an biya yuro miliyan 700 idan har ana son dan wasan yabar kungiyar hakan yasa ake ganin  babu kungiyar da a duniya zata iya biyan wannan kudin.

Da yake kaddamar da gasar La Liga ta kakar shekara ta 2020 zuwa 2021 ranar Litinin, shugaban La Liga Jabier Tebas ya ce bai “taba damuwa sosai” a kan aniyar Messi ta barin Barcelona a bazaar ba

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments