LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Ansu fati' ya karya tarihin shekaru 95 aqasar spain

Dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Ansu Fati, ya goge tarihin Sipaniya na shekaru 95 bayan ya zama dan wasa mai shekaru 17 da ya yi nasarar zura kwallo a raga ya yin wasansu na ranar Lahadi karkashin gasar cin kofin kasashen Turai da Spain ta lallasa kasar Ukraine da kwallaye 4 da nema.

Fati wanda ya zura kwallon ta sa a minti na 32 da fara wasa baya ga wannan tarihin ya kuma kafa tarihin zamowa dan wasan mafi karancin shekaru daya zura kwallo a gasar cin kofin zakarun Turai da kuma Laliga cikin kakar da ta gabata.

Ya yin wasan na ranar Lahadi ta sanadin Fati ne kasar ta Sipaniya ta samu bugun fenariti wanda dan wasan baya Sergio Ramos na Real Madrid ya zura kwallon tun a minti na 3 da fara wasa gabanin ya kara kwallo ta biyu a minti na 29.


Nasarar zura kwallayen biyu ta Ramos mai tsaron bayan Real Madrid ya nuna cewa yana da kwallaye 10 a jere da ya zurawa Sipaniya cikin wasanni 15 na baya-bayan nan ya yinda yake da jumullar kwallaye 23 dai dai da Afredo di Stefano.

Shima dai sabon dan wasan da Manchester City ta saya daga Balencia,  Ferran Torres da ya shiga fili bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ya rufewa Sipaniya da kwallonta ta 4 a minti na 84 da fara wasa.

Ansu Fati haifaffen kasar Guinea-Bissau da suka koma birnin Sebilla tare da mahaifansa tun yana da shekaru 6 nasarar tasa ta goge tarihin Juan Errazkuin wanda ya zura wa Sipaniya kwallo a shekarar 1925 yana da shekaru 18.


DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments