--
An amince sarkin Kano ya zama shugaban majalisar sarakuna na dindindin

An amince sarkin Kano ya zama shugaban majalisar sarakuna na dindindin

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da dokar naɗa Sarkin Kano a matsayin shugaban dindindin na Majalisar Sarakunan jihar kamar yadda gwamnatin jihar ta buƙata.

Gabanin kafa wannan doka, dokar masarautu ta jihar ta ce za’a riƙa yin karɓa-karɓa a shugabancin majalisar sarakuan jihar duk bayan shekara huɗu.

Sai dai gwamnatin jihar ta sauya dokar a maimakon tsarin na karba-karba tsakanin manyan sarakunan jihar guda biyar.

Shugaban masu rinjaye a majalisar dokokin jihar ta Kano Kabiru Hassan Dashe, ya shaida wa wakilimmu a Kano Khalifa Dokaji cewa dalilin sauya dokar shi ne cea masarautar Kano ta fi sauran masarautun jimawa da kuma shahara.

An gudanar da zaman majalisar ne ƙarƙashin jagorancin shugabanta Abdulaziz Garba Gafasa.

Haka zalika wani batu da shi ma ya saui amincewar majalisar shi ne na ƙara adadin masu zaɓar sarkin Kano daga huɗu zuwa biyar, inda aka bai wa sarautar Sarkin Dawaki Babba damar shiga jerin.

Duka wannan na cikin sauye-sauyen da Majalisar Dokoki ta yi wa dokar masarautun ta jihar Kano ta 2019 sakamakon ƙudirin da gwamna ya aike mata.

Rohoto Bbc Hausa

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "An amince sarkin Kano ya zama shugaban majalisar sarakuna na dindindin"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?