--
Matawalle ya bawa malamin Zamfara muƙami bayan karɓo shi daga gidan yari a Saudiyya

Matawalle ya bawa malamin Zamfara muƙami bayan karɓo shi daga gidan yari a Saudiyya

Gwamna Matawalle na jihar Zamfara ya naɗa Ibrahim Ibrahim a matsayin mataimakinsa na musamman bayan ceto shi daga gidan yari a Saudiyya.


An tsare shi ne na kimanin shekaru uku kan zarginsa da safarar miyagun kwayoyi. Daily Nigerian ta ruwaito cewa an tsare Ibrahim ne a shekarar 2017 a Saudiyya yayin da ya tafi umara kan wata jaka da ake zargin miyagun kwayoyi ke ciki.


Bayan kwashe shekaru uku ana shari'a, Ibrahim ya samu ƴanci sakamakon daukan lauyoyi da Gwamna Matawalle na Zamfara ya yi Attoney Janar na Najeriya.


Da ya ke sanar da nadin a ranar Talata, Kakakin gwamnan, Zailani Bappa cikin wata sanarwa ya ce Matawalle ya tarbi malamin a gidan gwamnati jim kedan bayan isarsa ƙasar.


A cewar Bappa, "Anyi haduwa mai sosa zuciya a yayin da Gwamnan ya mika malamin ga iyalansa da suka yi shekaru kusan hudu suna kewansa yayin da ya ke gidan yari yana jirar hukuncin kisa."


"Gwamnan bayan sanar da naɗin Hafeez Ibrahim a matsayin mataimakinsa na musamman ya ce gwamnati za ta cigaba da gwagwarmayar ƙwato hakkin duk wani ɗan jihar duk inda ya ke.


"Ya ce abinda ya faru da Hafeez darasi ne ga dukkan masu tafiye-tafiye zuwa kasashen waje su rika saka idanu a kan jakunkunansu," a cewar sanarwar.


Source: Legit.ng

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Matawalle ya bawa malamin Zamfara muƙami bayan karɓo shi daga gidan yari a Saudiyya "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?