LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Bayan tozarta dan jaridar Media Trust Fani-Kayode na neman diyyar biliyan shida

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama na Najeriya, Femi Fani-Kayode ya yi kurarin maka kamfanin Media Trust a kotu in ba ta biya shi diyyar Naira biliyan shida ba.

Fani-Kayode ya yi barazanar ce a cikin wasikar da ya aike wa kamfanin, ya kuma yada, kwana biyu bayan ya nemi gafara kan cin mutuncin da barazana ga lafiyar da ya yi wa wakilin kamfanin mai wallafa jaridar Daily Trust da Aminiya a garin Kalaba.

Bidiyon yadda Fani-Kayode ya yi wa dan jarida Eyo Charles ta jawo masa la’anta daga fadin duniya tare da kiransa da ya janye kalaman da barazanar da ya yi wa Mista Eyo Charles.

Tambayar da Charles ya yi wa tsohon ministan wanda ke zagayayen duba ayyukan gwamnoni -alhalhi shi ba jami’in gwamnati ba ne- ta bukaci sanin manufar yin hakan da kuma wanda ke daukar nauyin tafiye-tafiyen

Fani-Kayode ya dauki lokaci yana zagin Charles da yi barazanar taba lafiyarsa, har sai da aka sa baki, duk da cewa dan jaridar bai ce masa uffan ba.

‘Yan jarida da sauran masu sharhi sun yi amfani da kafofi iri-iri domin mayar masa da martani tare da caccakar abin da tsohon ministan ya yi.

Sau biyu tsohon ministan na bayyana nadama game da abin da yi wa Eyo Charles a matsayin abin kunya ga kansa da iyalansa tare da zubar da kimar kansa a idon masu ganin sa da mutunci.

Daga baya ya fito da sanarwar cewa wani sharhi da ke martani ga abin da ya yi wa Charles da aka wallafa a jaridar Daily Trust cin mutumci ne da zubar masa da kima.

Ya ce yana bukatar Media Trust ta biya shi ‘Naira biliyan shida da bai taka kara ya karya ba’, sannan ta janye sharhin da ya soke shi.

Yana kuma buƙata ta wallafa janye sharhin a wasu manyan jaridu biyu, sannan ta sasanta da shi.

Ya ce muddin jaridar ba ta yi haka ba, to ta kwana da shirin haduwa da shi a kotu.


Source: Aminiya Daily Trust

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments