--
Matar El-Rufai Na Neman A Ba Mace Sarautar Zazzau

Matar El-Rufai Na Neman A Ba Mace Sarautar Zazzau


Uwargidan Gwamnan Jihar Kaduna, Hadiza Isma El-Rufai, ta yi yi barkwanci game da ko mijinta zai nada mace a matsayin wadda za ta Jagoranci Masarautar Zazzau bayan rasuwar Sarki Shehu Idris.


Cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Juma’a 25 ga watan Satumba, Hadiza El-Rufai, ta yi tambaya ko hakan shi zai tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata.


“Bisa la’akari da tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata, shin akwai yiwuwar a sake samun wata sarauniya a Masarautar Zazzau makamanciyar Sarauniya Amina?”


Aminiya ta ruwaito cewa masu zaben Sarki na Masarautar Zazzau sun riga sun fara aikinsu na zaben sabon Sarkin Zazzau kamar yadda al’ada ta tana da.


Kebewar tasu na zuwa ne tun a washegarin ranar rasuwar Sarki na 18, Alhaji Shehu Idris, wanda ya rasu a ranar Lahadi 20 ga Satumba, 2020 bayan ya shafe shekara 45 a gadon sarauta.


Masu zaben Sarki a Masarautar Zazzau sun hada da Wazirin Zazzau, Ibrahim Aminu; Fagacin Zazzau, Umar Mohammed; Makama Karami, Mahmood Abbas; Limamin Juma’a, Dalhat Kasim; da kuma Limamin Kona, Sani Aliyu.


Bayan kammala aikinsu, masu zaben sarkin za su mika sunayen wadanda suka zaba ga Gwamnatin Jihar Kaduna domin bayyana wanda Allah Ya ba wa.


Source: Aminiya Daily Trust


DAGA: 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: 
bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Matar El-Rufai Na Neman A Ba Mace Sarautar Zazzau"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?