--
Jarrabawar WAEC: Yadda ƴan sandan Najeriya suka kama mutum 12 da satar amsa

Jarrabawar WAEC: Yadda ƴan sandan Najeriya suka kama mutum 12 da satar amsa


Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kama mutum 12 a wasu jihohin ƙasar, sakamakon zarginsu da taimakawa wurin satar amsa yayin zana jarrabawar kammala sakandare ta WAEC da aka kammala a 'yan kwanakin nan.


Kama mutanen na zuwa ne bayan dawo da ƙawance na musamman da ke tsakanin hukumar shirya jarrabawar ta WAEC da kuma 'yan sandan Najeriyar.


Binciken da rundunar 'yan sandan Najeriyar ta yi ta gano cewa waɗanda ake zargin, sun yi amfani da matsayinsu na masu sa ido kan jarrabawa wajen taimakawa domin satar amsa.


Dukkan mutanen da aka kama ɗin ƴan tsakanin shekaru 39 ne zuwa 52 daga jihohin ƙano da Ribas da Nasarawa da kuma Bauchi.


Babban sifeton 'yan sandan Najeriyar Mohammed Adamu ya yi kira ga iyayen yara da ɗalibai da masu ruwa da tsaki da ke shirya jarrabawa da su bayar da haɗin kai wurin kawo ƙarshen satar amsa a jarrabawar.



Babban Sufeton ya kuma tabbatarwa da hukumar WAEC cewa za a ci gaba da ba su goyon baya wajen daƙile al'adar satar amsa tare da hukunta ma su yi.


Dama tun a makon da aka fara jarrabawar a watan Agusta aka samu rahoton bazuwar satar amsar takardar adabin Ingilishi.


Hukumar Waec ɗin ce ta fallasa yadda wakilanta da masu kula da masu rubuta jarrabawar da kuma ɗalibai suka fitar da tambayoyi da amsoshin jarrabawar adabin Ingilishi tun kafin rubuta takardar.




Source: BBC HAUSA


DAGA: 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: 
bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Jarrabawar WAEC: Yadda ƴan sandan Najeriya suka kama mutum 12 da satar amsa"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?