--
Kalli Zafafan hotunan auren Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Buhari

Kalli Zafafan hotunan auren Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Buhari

 An daura auren Bashir Ahmad da sahibarsa Naeemah Bindawa, a ranar Juma'a, 25 ga watan Satumba, 2020 An daura auren ne a babban Masallacin Juma'a na G.R.A, jihar Katsina, inda dandazon mutane suka taru don shaida wannan aure 


Bashir Abdullahi El-Bash, aminin angon, ya wallafa zafafan hotunan auren hadimin shugaban kasar ta fuskar kafofin sada zumunta na zamani A ranar Juma'a, Allah ya kaddara, aka daura auren Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta fuskar kafofin sada zumunta, tare da amaryarsa, Naeemah.

Kalli Zafafan Hotunan Shagalin bikin Anan:












An daura auren Bashir da Naeemah a babban Masallacin G.R.A, jihar Katsina, inda dubunnan mutane suka taru don shaida wannan aure. Kamar yadda kuka sani burin kowasu masoya da suka tsinci kansu a cikin shau’kin so, shine ganin sun mallaki junansu ta hanyar kulla aure a tsakaninsu. 


Ko shakka babu hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad ya tsunduma sosai a cikin kaunar burin ransa, Naema. Bashir ya nuna farin ciki a yayinda yake shirin fita daga sahun gwauraye, domin ko a ranar Alhamis, 24 ga watan Satumba, sai da ya wallafa magana mai ratsa zuciya akai. 


A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter, mai ba Shugaban kasar shawara ya bayyana cewa a ranar Alhamis, 24 ga watan Satumba, ya sha shayinsa na karshe a matsayin gwauro. 


A wani labarin, Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da cewa sabbin mutane 125 ne suka kamu da cutar COVID-19 a kasar, inda aka samu jimillar mutane 57,849 da ke dauke da ita. Hukumar NCDC ta sanar da hakan a shafinta na Twitter @@NCDCgov a daren ranar Alhamis. 


Hukumar ta kuma sanar da cewa, mutane 49,098 suka warke sarai daga cutar kuma har an sallamesu daga asibiti, yayin da mutane 1,102 suka mutu sakamakon cutar. 


Source: Legit.ng

DAGA: 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: 
bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Kalli Zafafan hotunan auren Bashir Ahmad, hadimin shugaban kasa Buhari "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?