--
Da dumi-dumi: Roka rufta ta yi hadari ta fada rafi a Legas

Da dumi-dumi: Roka rufta ta yi hadari ta fada rafi a Legas


Roka dauke da yashi da mutane ta yi hadari a gadar Berger ta tsinduma cikin rafi a jihar Legas - Hadarin ya faru ne a daren ranar Juma'a 25 ga watan Satumban kamar yadda majiyoyi suka tabbatar 


Ma'aikatan hukumar agaji, 'yan sanda da direbobi suna can suna aikin ceto amma kawo yanzu ba a gano mutanen motar ba 


Mutane da dama sun bace sakamakon fadawa cikin rafin Epe da wata mota ta yi daga gadar Berger a jihar Legas. 


The Punch ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Juma'a 25 ga watan Satumban 2020. Hukumar Bada Agajin Gaggawa na jihar Legas ta tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Juma'a 


Shugaban sashin hulda da jama'a na LASEMA, Nosa Okunbor ya ce ana can ana bincike da nufin ceto mutanen. 


Ya ce, "Da isar su wurin da abin ya faru, sun gano cewa wata babbar mota mai taya shida makare da yashi ta fada cikin rafin. "Ba a tabbatar da adadin mutanen da ke cikin motar ba a lokacin da hadarin ya faru. 


"Tun safiyar yau, tawagar masu aikin ceto da suka hada da 'yan sanda da direbobi sun isa wurin suna ta kokarin ceto wadanda hadarin ya rista da su. "Kawo yanzu ba a tabbatar da mutuwar kowa ba." Karin bayani na nan tafe ... 


Source: Legit.ng

DAGA: 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: 
bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Da dumi-dumi: Roka rufta ta yi hadari ta fada rafi a Legas "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?