--
An bai wa ɓera lambar yabo saboda bajintarsa ta gano bama-bamai

An bai wa ɓera lambar yabo saboda bajintarsa ta gano bama-bamai

 


Magawa ya lashe lambar yabo ta zinare saboda bajintarsa ta gano bama-bamai a Cambodia


An bai wa wani bera dan asalin Afirka lambar yabo ta zinare saboda bajintar da ya nuna ta sansano bama-bamai da nakiyoyi da aka binne a karkashin kasa.


Beran mai suna Magawa ya sansano nakiyoyi 39 da abubuwan fashewa 28 a tsawon rayuwarsa ta aiki.


Kungiyar liktotin dabbobi ta Birtaniya PDSA ta mika wa beran lambar yabo ta zinare saboda "kare rayukan jama'a da ya yi lokacin yana aiki, da kuma kawar da baraguzan da aka binne nakiyoyi da ka iya fashewa a kasar Cambodia".


An yi kiyasin cewa akwai nakiyoyi miliyan shida binne a cikin kasa a Cambodia.


Lambar yabo ta zinaren ta PDSA na dauke da wasu kalamai da ke cewa an bai wa beran kyautar ce "Bisa jajircewarsa da mayar da hankali wurin aiki".


A cikin dabbobi 30 da aka bai wa lambar yabon, Magawa ne bera na farko.


Wata kungiyar kasar Belgium mai suna Apopo ce ta horas da beran mai shekara bakwai, wanda dan asalin kasar Tanzaniya ne kuma tana horas da dabbobi domin gano abubuwan fashewa da aka binne a karkashin kasa da kuma masu dauke da cutar tarin fuka a shekarun 1990.





Ana bai wa dabbobin lambar yabo bayan shekara daya idan aka gama horas da su.


"Bayar da wannan lambar yabon abin alfahari ne a gare mu," a cewar shugaban Apopo Christophe Cox a hirarsa da kamfanin dillancin labari na Press Association.


"Kuma hakan wani babban abu ne ga al'ummar Cambodia, da ma sauran mutane a duniya wadanda ke fama da fargabar zama a wuraren da aka binne nakiyoyi."



A cewar Apopo, Magawa - wanda aka haifa sannan ya girma a Tanzaniya - yana da nauyin 1.2kg da tsawon santimita 70.


Magawa yana iya zagaye fili irin wanda ake buga kwallon tennis cikin minti 20 - kuma Apopo ya ce hakan na iya daukar mutum mai rike da na'urar gano bama-bamai ko abubuwan fashewa tsakanin kwana daya zuwa kwana hudu.


Source: BBC HAUSA


DAGA: 


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: 
bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "An bai wa ɓera lambar yabo saboda bajintarsa ta gano bama-bamai"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?