--
Ku sani: Dalilin da ya sa gwamnatin Kano ta kama jarumin Kannywood, Naburaska

Ku sani: Dalilin da ya sa gwamnatin Kano ta kama jarumin Kannywood, Naburaska


Kwamitin kula da tsaftar muhalli da gwamnatin jihar Kano ta kafa, ta kama dan wasan Hausa, Mustapha Naburaska a karshen makon da ya gabata 


An gurfanar da jarumin a gaban kotun tafi-da-gidanka sakamakon keta dokar kwamitin na hana fita har sai karfe 10:00 na safe a duk ranar Asabar din karshen wata Sai dai jarumin na Kannywood ya ce rashin sani ne ya sa shi fitowa don halartan wata jana’iza 


Shahararren jarumin nan na Kannywood wanda ya kware a fannin barkwanci, Mustapha Naburaska, ya shiga tarkon kwamitin tsaftar muhalli da gwamnatin jihar Kano ta kafa a karshen makon da ya gabata. 


Jarumin wanda ya kasance mazaunin unguwar Tudun Wada da ke karamar hukumar Nasarawa ta jihar, ya gurfana a gaban kotun tafi-da-gidanka kan take dokar kwamitin tsaftar muhalli. 


Kwamitin dai ya hana fita har sai karfe 10:00 na dace a duk ranar Asabar ta karshen wata. 

A zantawa da yayi da manema labarai na gidan radiyon Freedom, Naburaska ya bayyana cewa rashin sani ne ya sanya shi fita domin halartan jana’izar wani rasuwa da aka yi. 


Ya kuma bayyana cewa a yanzu ya fahimci cewa tsaftar muhalli ta doke duk wani uzuri. An tattaro cewa Kotun ta ci tarar jarumin kudi naira dubu biyar kan keta dokar kwamitin na zama a gida don tsaftace muhalli. Amma kuma jarumin ya nemi sassauci inda ta yi masa rangwamen biyan naira dubu uku. 


A wani labarin kuma, Jarumin shirya fina-finai na Kannywood, Yakubu Mohammed, ya nuna dana sanin fitowa a wani fim din Nollywood na 'yan shi'a mai suna "Fatal Arrogance." 

Fitaccen jarumin nan na kudancin Najeriya, Pete Edochie ya fito a matsayin jagora a shirin fim din da akayi a jihar Enugu, wanda Anosike Kingsley Orji ya dauki nauyi. 


Source: legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Ku sani: Dalilin da ya sa gwamnatin Kano ta kama jarumin Kannywood, Naburaska "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?