--
Allah ke ciyarwa, zan cigaba da haihuwa - Mutumin da ke da 'ya'ya 19 (Bidiyo)

Allah ke ciyarwa, zan cigaba da haihuwa - Mutumin da ke da 'ya'ya 19 (Bidiyo)


Kukat Kamartum dan kauyen Riong'o, tare da matansa 3 da yara 19 suna zama a wani kango, ya ce yara arziki ne, kuma yana fatan yaransa su kara yawa Mutumin yace Ubangiji ne mai badawa, kuma bai taba damun kansa akan matsalolin rayuwa ba, kamar abinci, magani da ilimi 


Matan Kamartum 3 sunce basu da labarin ana shan maganin tsarin iyali, ko kuma akwai hanyoyin tsara iyali na musamman ba Wani mutumi mai shekaru 33, dan Baringo yana da yara 19, ya ce yara arziki ne nan gaba. Kukat Kamartum dan kauyen Riong'o, dake Baringo yana da mata 3 dake zaune tare, a wani dan kango inda suke kiwon tumaki da awaki 100. 


Kamartum yayi maganar nan ne ranar Lahadi, 27 ga watan Satumba, ranar tsara iyali ta duniya. Ya ce yana bukatar wasu yaran, saboda yana ganin zai iya azurcewa saboda yaran nan gaba. 


Yace, "Misali kana da yara mata 10 kuma aurensu ya tashi, za'a iya bada shanu 10 zuwa 15 saboda kowacce yarinya, kuma ana bada rakumai 4 akan kowacce yarinya, idan ka kirga, rakumai 40 kenan, kaga kuwa wannan dukiya ce mai yawa.


" Mutumin yace bai taba damuwa ba akan ciyar dasu, lafiyarsu da iliminsu, saboda Ubangiji ne yake yin komai. Da aka yi hira da matansa guda 3, cewa suka yi basu san ana tsarin iyali ba, balle har su san ana amfani da wasu magunguna. Su dai haihuwa kawai sukeyi, duk lokacin da ta kama. "Bamu taba jin labarin wani tsarin iyali ba," cewar uwargidan sa. 







Source: legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Allah ke ciyarwa, zan cigaba da haihuwa - Mutumin da ke da 'ya'ya 19 (Bidiyo) "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?