LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Kana taka Allah na tashi: Ango ya mutu kwanaki kadan bayan ya auri kyakkyawar amaryar shi


Wani saurayi dan Najeriya mai suna Rex Ebube Amatu, ya mutu bayan auren shi da wata budurwa sanadiyyar hatsarin babur 

An ruwaito cewa lamarin ya faru a Asaba  Mutane da yawa sun nuna jimaminsu akan wannan mutuwa tashi yayin da hotunanshi dana amaryar shi ke ta yawo a shafukan sadarwa Rana ce ta bakin ciki ga iyalan Rex Ebube Amatu, yayin da ya mutu a ranar Talata 8 ga watan Satumba, 2020, 

sakamakon hatsarin babur da ya rutsa da shi. A yadda rahotanni suka nuna Ebube ya mutu kwanaki kadan bayan auren shi da wata kyakkyawar budurwa. 

Mutumin dan asalin jihar Anambra ne. An ruwaito cewa hatsarin ya faru a Asaba a lokacin da yake komawa gidanshi dake Legas. Wani mai amfani da shafin sadarwa na Facebook mai suna Ben Chiedo ya ce lamarin ya faru yayin da katuwar mota ta bi ta kan angon. 

An ruwaito cewa tuni kyakkyawar matarshi na dauke da ciki. Mutane da yawa da suka ji wannan labari sun nuna rashin jin dadinsu akan abinda ya faru da wadannan ma'aurata. 

Ga dai wasu daga cikin abubuwan da mutane ke cewa kan wannan lamari: 

Wedded on 5th September 2020, Dead on September 8,2020 A newly wedded Nigerian young man who identified as Rex Ebube...

Posted by Ben Chiedo on Wednesday, 9 September 2020


Wani mai suna Kene Kay cewa yayi: "Menene haka, abin tausayi. Allah ka bawa 'yan uwa da matar wannan mutumi juriyar rashin shi, Allah kuma ya jikan shi. Amen." 


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments