LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Bidiyo: Ban taɓa sanin wani lokaci da al'ummar musulmi suka shiga halin ƙunci kamar yanzu ba - Goron-Dutse


Malamin addinin islama da ke Kano, Nasidi Goron-Dutse ya koka a kan mawuyacin halin rayuwa da musulmi suka shiga a yanzu 

Goron-Dutse ya ce tun da aka hallice shi bai taba ganin al'umma sun shiga irin halin kunci kamar wannan da ake ciki yanzu ba 

Malamin ya yi kira ga masu hali su rika tallafawa gajiyayyu da wadanda ba su da shi domin sadaka ta fi daraja inda aka bawa wanda ke cikin bukata 

Fitaccen malamin addinin musulunci mazaunin Kano, Nasidi Goron-Dutse ya koka a kan rayuwar ƙunci da ƴan Najeriya ke ciki musamman musulmi.

Duk da cewa malamin bai ambaci sunan Shugaba Muhammadu Buhari ba, ya nuna damuwarsa a kan yadda wahalhalu, hauhawan farashin kaya da rashin aikin yi ke ƙaruwa a ƙasar. 

A cikin gajeren faifan bidiyon malamin da ya yi magana cikin harshen Hausa, ya ce wannan shine lokaci mafi muni da ya taɓa ganin musulmin Najeriya sun shiga. 


"A dukkan rayuwa ta, ban taɓa ganin musulmin Najeriya cikin ƙunci wanda ya fi wannan ba. "Daga halitta ta, da na yi wayo har zuwa yanzu, ban taɓa sanin wani lokaci da musulmi suka shiga wani hali nairin wannan ƙunci, ni ban sani ba," 

kamar yadda malamin ya koka cikin bidiyon da ake kyautata zaton an ɗauka ne a lokacin da ya ke wa'azi a Kano. 

Malami ya cigaba da kira ga al'umma su taimakawa mabuƙata da masu ƙaramin ƙarfi komin ƙanƙantar abinda suke da shi inda ya ce, "babu wani lokaci da taimako ya fi buƙatuwa irin wannan ba". 

Ya cigaba da ƙarin bayani inda ya karanto hadisin Manzon Allah da ke cewa, "mafificiyar sadaka itace wadda aka bawa wanda ke cikin bukata," saboda haka ya yi kira ga masu hali su taimakawa mutane. 


Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments