--
Yadda Likitoci Suka Ceci Kunkuru Mai Shekara 79 A Sakkwato

Yadda Likitoci Suka Ceci Kunkuru Mai Shekara 79 A Sakkwato


Likitocin Dabbobi a Jihar Sokoto sun ceci rayuwar wani kunkuru mai shekara 79 da mota ta taka a garin Argungun na jihar Kebbi har ta tarwatsa kwaryar bayansa.


Dattijon kunkurun wanda mallakin mahaifin Jarman Argungu ne, Alhaji Suleiman Jarma, an ce a halin yanzu yana samun sauki.


Dakta Nura Abubakar, wanda ya jagoranci yi wa kunkuru tiyatar gaggawa ya ce sai da aka fara kai shi Asibitin Dabbobin garin Argungu kafin abun ya ci tura aka turo su Sokoto.


“Raunin da aka ji wa kunkurun na iya sanadiyyar mutuwarsa, kuma yana bukatar a gaggauta yi masa tiyata.

Ya ce kwaryar bayan kunkurun ta fashe a lokacin da aka kawo shi, “Nan da nan muka hada wadanda za su yi masa aiki daga Asibitin Dabbobin Jami’ar Usmanu Danfodio aka farfado da shi”, inji likitan.

Sadiq Suleiman, shi ya taka kunkurun da mota, kuma ya ce mahaifinsa ya gaji dabban ne daga wurin kakansa.

– Yadda abin ya faru –

Da ya ke bayanin yadda abun ya faru, Sadiq ya shaida wa wakilinmu a waya cewar yana sauri ne zai fita da mota bai san kunkurun na bayansa ba ya taka shi.

“Ina sauri ne inje wajen wani alkawarin da na yi, na yi ribas kansa, har kwaryar bayansa ta fashe.

“Na yi sauri na kai shi asibitin Dabbobi Argungun su kuma suka ce a zo da shi Sakkwato.

“Mun gode Allah da aka dinke kwaryar bayansa. Inda babu kwaryar sun yi amfani da wani abu mai kwari suka rife shi.

“Yanzu haka yana samun sauki sosai. Maganar da nake yi da kai ga shi nan yana wasa da yara”, inji Sadiq.

Ya kuma ce nauyin kunkurun zai kai buhun siminti daya, “ba na iya daukar sa sai dan uwana ya taimake ni”.

Ya ce, kunkurun na kakansa ne kafin mahaifinsa ya gaje shi bayan rasuwar kakansa.

“Kunkurun zai cika shekara 80 idan watan fabrailun 2021 ya kama”, in ji Sadiq.

Source: Aminiya Daily Trust

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yadda Likitoci Suka Ceci Kunkuru Mai Shekara 79 A Sakkwato"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?