LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Hukumar NAPTIP ta na zargin Mai kudi da bata ‘Yan mata 2 a Jihar Kano

Jami’an NATPIP sun yi ram da wani Mutumi da ya yi lalata da ‘Yan Mata biyu Wannan abu ya faru ne da wani ‘Dan kasuwa da kananan yara a garin Kano

Wanda ake zargi ya amsa laifinsa, ya ce N1200 ta raba shi da wadannan yara Jami’an hukumar NAPTIP masu yaki da safarar mutane a Najeriya ta tabbatar da kama wani mai kudi da ake zargi da yin lalata da ‘yan yara a jihar Kano.

Hukumar NAPTIP ta reshen jihar Kano ta bayyana cewa Alhaji Salisu Dala ya na hannunta, kuma ta na zargin shi da bata wasu kananan ‘yan mata su biyu.

Rahoton ya ce wannan mutumi, Salisu Dala wani ‘dan kasuwa ne mai shekaru 53 a garin Kano. Jaridar Daily Trust ta ce shugaban hukumar NAPTIP na shiyyar Kano da kewaye, Mista Shehu Umar shi ne ya tabbatar da labarin kama wannan mutumi.

Jami’ai sun cafke wannan mai kudi ne bayan labarin da su ka samu game da zargin da ake yi masa na lalata da yaran a ranar Juma’a 11 ga watan Satumba, 2020.

Kamar yadda jami’in hukumar yaki da safara da cin zarafin jama’a ya bayyanawa ‘yan jarida, wannan mutumi mai suna Salisu ya amsa laifin nasa da kansa.

“Wanda ake tuhuma ya amsa laifinsa na cewa ya yi lalata da yara biyu masu shekara 13 da 14.” “Ya shafe shekaru hudu ya na wannan danyen aiki da ‘yan kananan yara.” Inji Shehu Umar.

Wadannan yara biyu da su ka jawo asirin Salisu Dala ya tonu, su na saida ‘Fura’ da ‘Nono’ da ‘Dambu’ ne a Kano.

Wajen neman abin da zai rikesu, su ka fada tarkon wannan ‘dan kasuwa da ake zargin ya keta masu alfarma. Wannan mutumi ya ce ya ba ‘yan matan N500 da N700 ne domin ya yi amfani da su.

Bayan haka, hukumar ta ce ta ceto mutane 134 daga hannun masu safarar mutane a Kano a bana. An kama mutane 86 da ake zargin su na da hannu a wannan aiki.

Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments