LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Masu cewa akwai yunwa a Najeriya makaryata ne - Farouq Adamu Aliyu, babban na kusa da Buhari

Alkaluma daga kungiyoyin lissafin duniya sun nuna cewa Najeriya ta fi ko ina yunwa a duniya

Jihar Jigawa na daya daga cikin jihohi mafi yawa mabarata masu neman abinci Tsohon dan majalisar wakilai,

Adamu Aliyu, ya ce duk karya ne Daya daga cikin manyan na kusa da shugaba Muhammadu Buhari kuma tsohon dan majalisar wakilai, Farouq Adamu Aliyu, ya bayyana cewa duk masu cewa akwai yunwa a Najeriya makaryata ne.

Adamu Aliyu ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin hira da yake a shirin gari ya waye (Sunrise) na tashar Channels.

Dan siyasan yace a jiharsa na Jigawa, babu yunwa kuma hakazalika sauran jihohin Najeriya. Yayinda aka yi masa tambaya da rahoton dake nuna cewa Najeriya ce cibiyar yunwa a duniya, Adamu Aliyu yace:

"Ban tunanin gaskiya ne saboda jihata da sauran jihohin Najeriya mutane basu jin yunwa." "Karya ce kawai, a kasar nan babu yunwa."

Shugaban kasar ya bukaci yan Najeriya da su ci abunda ake shukawa a kasar. Ya fadin hakan ne da yake amsa tambayoyi a filin Jirgin sama na Sir Ahmadu Bello, Birnin Kebbi a lokacin wani rangadi don ganin irin barnar da ambaliyar ruwa ya yi a jihar Kebbi.


Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin ministan noma, Mohammed Sabo Nanono, ya ce a shirye gwamnatin tarayya take ta ba manoma tallafi domin bunkasa harkar noma.

Source: Legit.ng


LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments