--
FG ta buɗe sabon shafin yanar gizo, ta ƙirƙiri manhajar wayar hannu - Pantami

FG ta buɗe sabon shafin yanar gizo, ta ƙirƙiri manhajar wayar hannu - Pantami


Gwamnatin tarayya ta kaddamar da sabon shafin yanar gizo tare da manhajar wayar hannu, domin bunkasa tattalin arziki ta kafar yanar gizo 


Dr. Isa Pantami, ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani (FMCDE) ya kaddamar da shafin tare da manhajar mai suna 'Digital Nigeria' 


Pantami ya bunkaci 'yan Nigeria da su yi rejista a wadannan shafukan; https://digitalnigeria.gov.ng; da kuma https://academy.nitda.gov.ng/ Gwamnatin tarayya ta kaddamar da sabon shafin yanar gizo tare da manhajar wayar hannu, a shirin mayar da ayyukan gwamnatin Nigeria a tsarin yanar gizo. 


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da wannan shiri na Nigeria a yanar gizo (DNP) a ranar 19 ga watan Maris, 2020. Dr. Isa Pantami, ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani (FMCDE) ya kaddamar da shafin tare da manhajar a ranar Litinin, ta hanyar bidiyo a yanar gizo, a birnin tarayya Abuja. 


Pantami ya ce wannan na daga cikin yunkurin gwamnati na bunkasa masu kirkira da kasuwanci na zamani, ta hanyar ilimantar da su kan yin harkalloli ta yanar gizo don samun kudi. 


Ya bayyana cewa shirin Nigeria a yanar gizo na daga cikin shiri da tsarin gwamnati na daga dajarar tattalin arziki ta hanyar yanar gizo, wanda shi ya kaddamar da shirin. 


Pantami ya ce ma'aikatar na hadaka da cibiyoyin kasashen waje da suka hada da bankin bunkasa Afrika (AFDB) da kuma kamfanin Microsoft, domin ganin 'yan Nigeria na cin moriyar yanar gizo a cikin gidajensu. Sai dai Ministan, ya ce gwamnati za ta fi mayar da hankali kan bunkasa mutanen da suke da basirar kasuwanci ta yanar gizo, ba wai la'akari da takardun da mutum ya mallaka ba. 


"Muna kokarin ganin cewa mun mayar da hankali kan kwarewa da fasaha, ba zamu yi la'akari da takardun karatu ba, ma damar ba ka da fasaha da kwarewa, ba zamu bunkasa ka ba. "Ana amfani da takardun Degree ne kawai don daga darajar fasaha da kwarewa, amma abunda aka fi mayar da hankali akanshi a fadin duniya, shine kwarewar mutum da fasaharsa. 


"Wannan shirin zai taimaka ainun wajen kara horaswa da kuma bunkasa mutanen da ke da kwarewa da fasahar amfani da yanar gizo, don ci gaban tattalin arziki. "Digital Nigeria" manhajar wayar hannu na a rumbun PlayStore da Apple Store, wanda zai baiwa 'yan Nigeria damar shiga darussa na kimiyar yanar gizo, su koyi karatu a gidajensu," a cewar sa. 


Pantami ya bunkaci 'yan Nigeria da su amfani da wannan damar wajen yi wa kawunansu rejista a wadannan shafukan; https://digitalnigeria.gov.ng; da kuma https://academy.nitda.gov.ng/ "Shafukan za su bayar da cikakken bayani yadda za ayi rejista da kuma sauke manhajar da ta dace. 


"Za mu ci gaba da sabunta darussan domin su dace da zamani. Shirin Digital Nigeria zai samar da muhallin da 'yan Nigeria za su bunkasa iliminsu kan na'ura mai kwakwalwa da yanar gizo." 


Wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Farfesa Umar Danbatta, mataimakin shugaban hukumar NCC, da kuma Farfesa Mohammed Abubakar, shugaban kamfanin Galaxy Backbone (GBB). 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "FG ta buɗe sabon shafin yanar gizo, ta ƙirƙiri manhajar wayar hannu - Pantami "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?