--
Barakar da Najeriya ke ciki a yanzu za ta iya tarwatsa ta - Osinbajo

Barakar da Najeriya ke ciki a yanzu za ta iya tarwatsa ta - Osinbajo


Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasar Najeriya, ya ce akwai bukatar toshe barakar da ke kunno kai 


Ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin shagalin cikar Najeriya shakaru 60 da samun 'yancin kai 


Ya sanar da cewa, rashin toshe barakar da ke kunno kai na iya tarwatsa kasar Najeriya matukar ba a dauka mataki ba Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya ce akwai yuwuwar tarwatsewar Najeriya idan ba'ayi kokarin toshe barakar dake kunno kai ba. 


Yace akwai wadanda zasu iya yunkurin hana toshe barakar, amma idan aka jajirce kuma aka dage da addu'a za'a iya cimma gaci. Osinbajo yayi wannan jan kunnen ne a ranar Lahadi a Abuja a wata tattaunawa da aka yi da shi, saboda shiryawa shagalin cika shekaru 60 da samun 'yancin kai na Najeriya. 


Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ne ya wakilci mataimakin shugaban kasar, The Punch ta wallafa. 


Cikin mutanen da suka samu damar halarta har da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan; kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila; shugaban ma'aikatan tarayya; Folshade Yemi-Esan; manyan sakatarorin gwamnati, mayakan tsaro da sauran manyan mutane. 


Source: Legit.ng

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 

KU BIYOMU A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 
@FACEBOOK:

@TWITTER: 

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: 

0 Response to "Barakar da Najeriya ke ciki a yanzu za ta iya tarwatsa ta - Osinbajo "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?