LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Da duminsa: Yan bindiga sun kai farmaki Abuja, sun yi awon gaba da mutane da dama


Yan bindiga sun kai farmaki garin Tungan Maje, waje-wajen birnin tarayya Abuja, inda sukayi awon gaba da mutane da ba'a san yawansu ba har yanzu. Premium Times ta samu labari daga wani mazaunin garin cewa akalla mutane 20 aka sace bayan dogon lokaci ana harbe-harbe a cikin garin. 


Kakakin hukumar yan sandan birnin tarayya, Anguri Manzah ya bayyanawa wakilin Premium Times cewa bai yi jawabi a kai ba tukun amma yana shirin yi. Bai tabbatar da adadin wadanda aka sace ba, ko kuma akwai wadanda suka mutu ko suka samu rauni. 


Wani mazaunin unguwar da aka sakaye sunansa ya ce sun fara jin harbe-harben bindiga ne misalin karfe 12:15 na dare kuma sai da aka kwashe awa daya ana yi. Ya ce an galabi yan bangan dake garin. "Bamu yi bacci ba gaba daya cikin dare. Sai da safen nan yan banga suka fada mana cewa an yi awon gaba da kimanin mutane 20," Yace 


Wannan harin ya biyo bayan da Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa yan ta'addan Boko Haram na shirin kai farmaki babbar birnin tarayya Abuja, da jihohin da ke makwabtaka. Gwamnatin ta ce yan ta'addan na shirin kai hari ne wasu wurare na musamman a birnin tarayya kuma tuni sun kafa mabuya guda biyar a Abuja. 


A cewar wata takardar da Kontrollan hukumar hana fasa kwabri wato kwastam, H.A Sabo, ya saki ranar 20 ga Agusta, 2020, ya bukaci dukkan hafsoshin su kasance cikin farga. Takardar tace: "Labarin da Kontrola Janar na hukumar Kwastam ya samu ya nuna cewa akwai mabuyan yan ta'addan Boko Haram a ciki da wajen birnin tarayya Abuja."


"Karin bayani ya nuna cewa suna shirin kai hari wasu wurare cikin birnin." "Saboda haka, ana sanar da ku kasance cikin tsaro a koda yaushe. Ku tabbatar labarin nan ya yadu." 


Source: Legit.ng


DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments