--
CORONA: Sama Da Aure Dari Uku Ne Ya Mutu A Kano A Lokacin Dokar Kulle, Cewar Hukumar Hisbah

CORONA: Sama Da Aure Dari Uku Ne Ya Mutu A Kano A Lokacin Dokar Kulle, Cewar Hukumar Hisbah

Hukumar Hisba ta Kano ta koka game da karuwar yawaitar mutuwar aure a tsakanin ma’aurata a Kano, tana mai cewa a lokacin dokar zaman kulle kadai an saki matan aure   guda dari uku da hudu a nan jihar Kano.

Babban Daraktan Hukumar Hisba ta jihar Kano, Dr. Aliyu Musa Kibiya shine ya bada wadannan alkaluma, sa’ilin da yake hira  da manema labarai game da aiyukan hukumar Hisbah a Kano.

Dr. Aliyu ya  baiyana damuwar sa game da yadda tun lokacin da aka samu barkewar  annobar corona a Kano zuwa yanzu, aka samu salwantar aure har guda dari uku da hudu. Daga nan sai ya yi kira ga ma’aurata da su  kasance masu hakuri da yin gaskiya a  tsakanin su domin samun raguwar sakin aure  a jihar Kano.

Babban Daraktan ya ce a makon da ya gabata  kadai sun karbi korafe –korafe akan  zamantakewar aure guda 46, inda daga cikinsu suka samu nasarar warware guda  33  yayin da  guda uku kuma aka tura su zuwa  kotu.

Source: Rariya Daga Abdulrashid Abdullahi, Kano

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "CORONA: Sama Da Aure Dari Uku Ne Ya Mutu A Kano A Lokacin Dokar Kulle, Cewar Hukumar Hisbah"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?