--
Amfanin Lallen Gargajiya Da Ya Kamata Ku Sani

Amfanin Lallen Gargajiya Da Ya Kamata Ku Sani

Lalle na daga cikin kayan abubuwan da ake amfani da wajen ado da zayyana a jikin dan Adam.

Baya ga kwalliya da ake yi da shi, lalle na dauke da sinadarai masu amfani masu tarin yawa.

Ga kadan daga cikin amfanin lalle da muka zakulo muku:

Ciwon kafa: Yin lalle na rage ciwon kafa. A kwaba lalle da ruwa ya yi kauri, a shafa wa kafar na tsayon lokacin da ake bukata sannan a wanke. Yin haka na rage radadi da zugin da ke damun mutun a kafarsa.

Dattin ciki: Shan ruwan lalle na wanke dattin dake ciki. Idan aka jiga lalle da ruwa aka tace, sai a sha ruwan daidai gwargwado. Yin hakan na wanke dattin ciki.

Gyaran fata: Ana amfani da lalle wajen gyara fatar jiki da kawar da datti da kuma sanya fata haske mai kyau. Domin haka, sai a zuba lalle da ruwa a rika wanka da ruwa lallen akalla so daya a rana.

Fatar fuska: Lalle na sa fuska ta yi laushi da haske. Bayan an kwaba lallen da kauri a rika goga fuskar ta ita. Bayan minti 20 zuwa 30 sai a wanke fuskar da ruwa. Za a iya yi sau daya zuwa uku a rana.

Kurajen fuska: Ga masu fama da kurajen ‘pimples’ sai su kwaba lalle da ruwan lemon tsami ya yi kauri suka rika shafa kwabin a fuskar. Zuwa wani lokaci pimples din za su bace.

Amosanin kai: Ana a wanke gashin kai da ruwan lalle domin maganin amosarin gashi. Ana yin hakan ne ta hanyar kwaba lalle a ruwa ya yi dan ruwa-ruwa sannan a jika gashin a cikin ruwan. Bayan minti 20 sai a wanke kan. Yawan yin hakan na kashe amosarin kai.

Gyambon yatsa: Masu gyambon yatsa (dankankare) na amfani da lalle wajen neman sauki. Akan kwaba shi a sanya a wurin da ke da gyambon a yatsar don neman waraka ko busar da shi.
Kwalliyar gashi: Maza da mata na amfanin da shi domin kwaliya a gashin kansu da kuma gemu. Domin yin hakan, sai da a kwaba lalle da ruwa a shafa a waurin da ake bukata na ‘yan mintoci sannan a wanke.

Zayyana fata: Ana kuma amfani da lalle wajen yin ado ta hanyar zayyana a fatar ji. Akan kwaba lalle ta yi kauri, sannna a lika leda mai dauke da nau’in zayyanar da za a yi a fatar, sannan a shafa lallen a sama. Daga nan sai a bar shi ya yi awanni kafin a wanke. Ana kuma iya yin zayyarar kai tsaye da kwababben lallen ba tare da sanya ledar ado ba.
Wasu daga cikin amfanin lalle ke nan ga dan Adam. Da fatar an karu.

Source: Aminiya Daily Trust

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Amfanin Lallen Gargajiya Da Ya Kamata Ku Sani"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?