LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Zamfara: Kotu ta yankewa soja hukuncin shekaru 55 a kan kisan farar hula

Wata kotun sojoji da ke zama a Abuja a ranar Laraba ta yanke wa wani soja hukuncin shekaru 55 a gidan yari a kan kisan kai, balle wa tare da sata. 


Sojan mai mukamin Lance Corporal, an zargesa da kashe wani mutum mai suna Bello Abdullahi Aliyu tare da kwace masa mota a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara. Lance Corporal Ibrahim Babangida ya aikata laifin ne a 2014.


Aliyu a wancan lokacin ma'aikacin kungiyar kiwon lafiya ta duniya ne a jihar. An zargi kofur Babangida da satar waya da kudi N600,000 daga wurin mutane da dama a lokuta mabambamta. 


Solacebase ta ruwaito cewa shugaban GMC, Manjo Janar Priye Fakrogha yayin karanta hukuncin bayan sauraron bayanai daga masu gurfanarwa da masu kare kansu, ya ce wanda aka kama da laifin an yanke masa hukuncin shekaru 40 a gidan yari saboda kisan kai. 


Janar Fakrogha ya kara da cewa, Babangida zai yi zaman gidan yari na shekaru biyar sakamakon kin amsa laifinsa da yayi har sau uku. PRNigeria ta gano cewa, hukuncin GCM din zai tabbata ne bayan hukumar sojin kasa ta Najeriya ta amince da shi. 

SOURCE: LEGIT.NG


DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

 

Post a comment

0 Comments