LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Ragon maza: 'Ina yawan shan duka a wurin mata ta' - Miji mai neman saki

 

Wani dan kasuwa mai suna Gbade Olaniyi ya shigar da karar matarsa, Olubunmi, a gaban wata kotun gargajiya da ke Ile-Tuntun a garin Ibadan domin neman a raba aurensu saboda dukan da ya ke yawan sha a hannunta. 


Da ya ke bayar da shaida a gaban kotu, Olaniyi ya bayyana cewa; "mata ta tafi karfina. Ta rabani da abokaina da 'yan uwana. "Duk lokacin da wani karamin sabani ya shiga tsakanimu sai ta zabgeni da mari. Ko a ranar 2 ga watan Agusta, kimanin kwanaki goma da suka gabata, sai da ta mareni, 


ta yi min rauni da farcen hannunta. "Ta ce tana yi min hakan ne saboda ba na fada mata daga inda nake duk lokacin da ta tambayeni idan na dawo gida.


"Ta wulakanta aure ta hanyar wofantar da nauyin da ke wuyanta. Ta kan bar gida, ta yi kwanaki ko watanni, ba tare da na san inda take ba, ba kuma tare da wani dalili ba," a cewarsa. Matar ta amince da bukatar mijin ta neman a raba aurensu. 


"Mai girma mai shari'a, mijina ya zama fakiri, yaranmu ko suturar kirki basu da ita. "Wasu lokutan na kan bar gidansa saboda ya gaza daukan nauyina, hatta a lokutan da na ke da juna biyu. "Na mareshi ne saboda na samu labarin yana lalata da wata karamar kwaila da ke zaune kusa da gidanmu. 


"Na samu labarin yana aikata hakan ne saboda 'yar uwar yarinyar ta zo har gida domin yi masa gargadi. Sannan ina da shaidar sakon katin waya da na soyayya da ya ke aika mata. Har Otal su ke tafiya tare," kamar yadda Olubunmi ta shaidawa kotu. Alkalin kotun, Cif Henry Agbaje, ya bayyana cewa ma'auratan sun gaza gabatar da gamsassun hujjoji, a saboda haka akwai bukatar su kara gabatar da shaidunsu da karin hujjoji. Ya bukaci kowannensu ya zo da magabatansa a zaman kotun na gaba da za a yi domin yanke yanke hukunci a ranar 19 ga watan Agusta. 


NAN 

SOURCE: LEGIT.NG


DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

 


Post a comment

0 Comments