--
Yanzu-yanzu: Hukumar DSS ta saki Obadiah Mailafiya

Yanzu-yanzu: Hukumar DSS ta saki Obadiah Mailafiya

Hukumar tsaron farin kaya watau DSS, ta saki Dr Obadiah Mailafiya bayan sa'o'i bakwai ana yi masa tambayoyi. Vanguard ta ruwaito cewa uwargidar Mailafiya, Margaret, ta kai kuka bisa cigaba da tsareshi. 

Jiya mun kawo muku rahoton cewa Hukumar DSS sammaceshi ne kan jawabin da yayi inda ya bayyana cewa daya daga cikin tubabbun yan Boko Haram da aka saki ya fada masa cewa wani gwamnan Arewa ne shugaban yan Boko Haram.

Dr Obadiah Mailafia ya ce shi da wasu masu ruwa da tsaki a yankin sun tattauna da tubabbun yan bindiga kuma sun fada musu daya daga cikin gwamnonin arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya. Mailafia ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Nigeria Info FM a ranar 8 ga watan Agustan shekarar 2O2O. 

Kalamansa; "Bari inyi bayanin wasu abubuwa domin wasu daga cikin mu muna binciken sirri mu ma. Mun gana da wasu daga cikin yan bindiga da suka tuba, daya ko biyu daga cikinsu. Mun tattauna ba sau daya ba, ba biyu ba. 

"Sun fada mana cewa daya daga cikin gwamnonin jihohin arewa ne kwamandan Boko Haram a Najeriya. "Boko Haram da yan bindiga duk daya ne a Najeriya. Suna da tsari mai sarkakiya da wuyan gane wa. "A lokacin kullen korona, jiragen su na ta zirga zirga suna kai makamakai da kudade zuwa sassa daban daban a kasar kamar babu dokar kulle. 

"Sun riga sun isa kudu. Babu inda babu su. Sun ce mana idan sun gama kai hare hare kauyuka, za su shiga mataki na biyu. Mataki na biyu shine za su fara kai hari birane suna zuwa gidan manyan mutane suna kashe su. Ina tabbatar maka, wannan shine tsarin su.

"Zuwa shekarar 2022, suna son su fara yakin basasa a Najeriya. Kada ku dauka abinda na ke fadi wasa ne. Na yi digiri na ta 3 a Jami’ar Oxford. Ni kuma kwararren ma’aikacin banki ne. Ba mu fadin shashanci. 

"Kada kayi wasa da abinda na ke fada maka." Da aka tambaye shi ko gwamnan da ya ambata da farko, tsohon gwamna ne ko mai ci yanzu, Obadiah ya ce. "Yana kan mulki yanzu. Ya ce daya daga cikin gwamnonin ne kwamandan Boko Haram a Najeriya kuma ba kudi suke nema ba, suna da isassun kudi."

 Kalli bidiyon: 



SOURCE: LEGIT.NG


DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

 

0 Response to "Yanzu-yanzu: Hukumar DSS ta saki Obadiah Mailafiya "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?