--
Yanzu yanzu: Buhari yana ganawa da gwamnoni da shugabannin tsaro

Yanzu yanzu: Buhari yana ganawa da gwamnoni da shugabannin tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a halin yanzu yana ganawa da wasu wakilan kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, da shugbannin hukumomin tsaro na kasar a fadarsa da ke Abuja. Taron na da alaka da kokarin da gwamnatin ke yi na magance matsalar tabarbarewar tsaro a wasu sassan kasar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo; Sakataren gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da Mai bawa Shugaban kasa shawara ta fanin tsaro, Babagana Monguna suma sun hallarci taron.

Kazalika, sauran shugabannin rundunar sojoji da hukumomin tsaro na kasar suma sun hallarci taron. Wasu daga cikin gwamnonin da za su hallarci taron ta intanet sun hada da gwmanan Kogi, Yahaya Bello;

Douye Diri na jihar Bayelsa; Babagana Zulum na jihar Borno; David Umahi na jihar Ebonyi da Babajide Sanwo Olu na jihar Legas.

A ranar Litinin, Buhari ya gana da gwamnonin jihohin Arewa maso Gabas game dai da batun tsaron.

SOURCE: LEGIT.NG 

Ku saurari cikkaken rahoton ... 

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yanzu yanzu: Buhari yana ganawa da gwamnoni da shugabannin tsaro "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?