LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yanzu-yanzu: Mun samu rigakafin Coronavirus ta farko a duniya, an yi 'diyata alluran - Shugaban kasan Rasha

An samu rigakafin cutar Korona ta farko a duniya - Shugaban kasan Rasha ya ce an yiwa 'yar cikinsa
Ya tabbatarwa duniya cewa rigakafin na samar da garkuwa mai karfi daga Coronavirus Bayan watanni takwas da bullarta a duniya, an samu rigakafin cutar Coronavirus na farko a duniya,

Shugaban kasar jamhurriyar Rasha, Vladimir Putin, ya alanta. Valdimir Putin ya ce ya amince da fara yiwa mutane alluran rigakafin saboda yana aiki sosai, kuma tuni an yiwa diyarsa. A cewar Reuters, Rasha ce kasa ta farko a duniya da ta bada umurnin fara amfani da rigakafi a duniya,

watanni biyu kacal bayan fara gwaji. Yayinda yake magana a wata ganawa, Putin ya ce cibiyar Gamaleya ta kasar ce ta samar da rigakafin kuma yana bada kariya daga cutar Korona.

"Na san rigakafin na aiki sosai, yana samar da garkuwan jiki mai karfi, kuma ina jaddada CEWA, rigakafin ya zarce duka matakan gwaji,"

Putin ya fadi. Kawo ranar 31 ga Yuli, 2020, kungiyar lafiyar duniya WHO ta samu mutane 26 da ake yiwa gwajin rigakafin a mataki na karshe kuma ana gwajin mutane 139 a mataki na kusa da karshe. Daga cikin wuraren da ake gwajin akwai jami'ar Oxford/AstraZeneca da kamfanin Pfizer.

SOURCE LEGIT.NG


DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments