LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Duniya juyi: Yadda tsohon dan majalisa ya koma kwasar bola (Hotuna)

Oluomo Segun Olulade wanda aka fi sani da Eleniyan, tsohon dan majalisa ne mai wakiltar mazabar Epe ta II, wanda ke da kamfanin kwasar shara

A wata wallafa da yayi a shafinsa na Instagram, tsohon dan majalisar ya bayyana yaddda ya gyara kamfaninsa da amfanin mayar da hankali

Segun ya yi dan majalisar jihar a Legas har sau biyu amma yanzu yana da kamfanin kwasar bola Tsohon dan majalisa, Oluomo Segun Olulade, wanda ya wakilci mazabar Epe ta II, ya koma kasuwancin kwashe shara.

Kamar yadda ya sanar, an haifesa a ranar 20 ga watan Yulin 1971 kuma ya fara karatunsa a Epe kafin ya karasa jami'ar jihar Legas inda ya yi digirinsa a kan tsumi da tattali. Kasuwancinsa a yanzu na kwasar bola, ya fara ne daga yadda yake son gyaran muhalli da kuma shawo kan matsalolinsa.

Bayan manyan nasarorin da ya samu a fannin tsaftace muhalli, ya fada harkar siyasa inda ya yi wakilci a majalisar jihar har sau biyu. Kamar yadda ya nuna, shine dan majalisa na farko da ya fara koyarwa ta rediyo tun daga tushe.

A ranar Litinin, 10 ga watan Augusta, ya wallafa hotuna da bayani a kan kamfaninsa na kwasar shara inda yayi magana a kan jajircewa. Hotunan da ya wallafa a shafinsa na Instagram ya bayyana tare da daya daga cikin manyan motocin kamfaninsa na dibar shara.

SOURCE:  LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments