LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yadda dan sanda ya yi kisa saboda Naira 50

Wani sufeton dan sanda ya rasa aikinsa saboba kashe wani matashin tela dan shekara 20, kan cin hanci na Naira 50.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Osun ta ce dukan da Sufeta Ago Egharevbe ya yi wa Ayomide da gindin bindiga ta kai ga kwantar da matashin a gadon asibiti har ya ce ga garinku.

Dan uwan mamacin, Oladimeji Wasiu, ya ce lamarin ya faru ne wani shingen binciken ababan hawa, a lokacin da shi da dan uwansa suke dawowa daga Osogbo zuwa Iragbiji a kan babur domin yin bikin Babbar Sallah a gida.

Wasiu ya ce “daya daga cikin jami’an ya fusata inda ya nemi Ayomide ya ba su Naira 50 a matsayin na goyo, amma Ayomide ya yi jinkirin fito da kudin.

“Bayan da ma’aikacin ya gano akwai kudi masu yawa a tattare da Ayomide, sai ya hau dokin zuciya inda ya buge shi da gindin bindiga, wanda hakan ya tilasta duk mu biyun muka zube a kasa kuma Ayomide ya fita daga hayyacinsa.

“Ganin haka ya sanya sauran jami’an uku suka tsere abinsu,” inji shi.

Sanarwar da Kakakin rundunar, SP Opalola Yemisi ta fitar ranar Lahadi, ta ce faruwar lamarin ke da wuya aka yi gaggawar damke Sufeta Egharevbe.

Yemisi ta ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Undie Adie, ya ba wa Sufeto Janar na ’Yan Sanda shawarar sallamar jami’in saboda mummunar ta’asar da ya aikata.

Ta ce rundunar ba ta lamuntar rashin da’a, zalunci ko keta dokar aiki daga kowane ma’aikaci da ke karkashinta.

Yayin da take jajenta wa ’yan uwan mamacin, jami’ar Yemisi ta kara da cewa za a gurfanar da Sufeta Egharevbe gaban kuliya a ranar Litinin.

Da yake ba da tabbaci, Mista Popoola Adebayo, wanda shi ne ubangidan mamacin, ya ce mutuwa yaron nasa Ayomide ya rasu ne bayan ya shafe kwanaki biyar ba tare da sanin kowaye a kansa ba.


SOURCE:  AMINIYA DAILY TRUST

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments