LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Yahaya Sharif-Aminu: Tarihin mutumin da za a kashe saboda ya yi ɓatanci ga Annabi a Kano

Ranar Litinin wata babbar kotun jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yanke wa wani matashi mai shekara 22 hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa yin kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad S.A.W.

BBC ta lalubo tarihin matasin kamar haka:

An haifi Yahaya Sharif-Aminu a unguwar Sharifai, a gidan Mallam Aminu Sha'aibu Sharifai wanda malamin addini ne kuma mai yabon Manzon Allah SAW.

Ya fara karatu a makarantar firamaren 'yan awaki da ke unguwar Koki, sannan ya wuce karamar sakandire a GATC Gwale daga aji 1 zuwa 3.

Bayan ya kammala sakandire ne sai ya bar karatu ya koma sana'ar saye da sayarwa ta takalma.

Haka kuma ya yi karatun addinin Islama a gaban mahaifinsa, wanda ya yi da'awa a jawabin da ya gabatar a gaban kotu na cewar mahaifin nasa shi ne shehinsa.

Ya ce shi dan kungiyar Faira ne a darikar Tijjaniya kuma yana gabatar da salloli biyar a kullum.

Ya hada wani dandali na Whatsapp da ya yi wa lakabi da Umma Abiha, wato dandalin masoya 'yar manzon Allah SAW.

A ranar Asabar 29 ga watan Fabrairu, 2020, a lokacin da suke hirar addini a dandalin aka sami wani ya soki darikar Tijjaniya yana mai zargin suna tafiya dai dai a inda shi kuma ya nadi muryarsa ta (Voice note) inda yayi kalaman batanci ga Manzan Allah SAW, wanda ya yi su ne kan an soki darikar Tijjaniya da yake bi.

A inda bayan yin kalaman nasa ne sai ya siyar da wayar sa ya yi kudin mota zuwa Jigawa don gudun abin da zai je ya dawo.

Matashiya

Sakamakon wadannan kalamai na batanci da ya yi, wata babbar kotun Jihar Kano ta yanke wa matashin hukuncin kisa ta hanyar rataya

Baba Jibo Ibrahim, Kakakin Babbar Kotun Kano, shi ne ya tabbatar wa BBC da hakan, inda ya ce dukkaninsu suna da damar ɗaukaka ƙara.

"An yanke wa matashin mai suna Yahaya Aminu Sharif hukuncin kisa ne sakamakon danganta Annabi S.A.W. da ya yi da shirka," in ji Jibo Ibrahim.

"A halin yanzu za a rataye shi har sai ya mutu, kamar yadda sashe na 382 (b) na kundin shari'ar Jihar Kano ta shekara ta 2000 ta tanada.

Tun a watan Maris ne wasu matasa suka yi sun yi zanga-zangar neman a hukunta wani Yahaya Sharif-Aminu, wanda suka zarga da yi wa Annabi Muhammad S.A.W batanci.

Matasan sun yi cincirundo ne a gaban ofishin hukumar Hisbah, inda kwamandan hukumar ya tarbe su.

Kafin lokacin, wasu fusatattun matasa suka far wa gidan mahaifan mawakin a unguwar Sharifai da ke kwaryar birnin Kano tare da lalata abin da ke ciki.


SOURCE:  BBCHAUSA

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments