LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Wata mata ta ce tana da asirin amshe kudaden attajirai

Bi Stella ta ce ta fara harka da masu dadiro ne bayan iyayen ta sun rasu - Ta ce kanwar mahaifiyarta ce ta koya mata zuwa gidajen rawan badala da yadda za ta janyo hankulan maza

Stella ta yi ikirarin cewa tana da asirin mallake attajirai kuma ta kashe kudinsa ta yadda ta ga dama Bi stella, wata mata da ta dena karuwanci ta ce tana da asiri da ta ke amfani da shi domin janyo hankulan attajirai a duk lokacin da ta ke so.

Matar wadda ta ce wahalhalun rayuwa ne yasa ta fada irin wancan rayuwar ta ce kanwar mahaifiyarta ce ta koyar da ita harkar wadda a lokacin ya zama hanyar cin abincin ta.

Da ake hira da ita a Radio Jambo, matar ta yi bayanin cewa ita da attajirai kawai ta ke harka da su cikinsu har da ministoci da wasu masu arziki.

"Ban taba zuwa gefen titi ina tallata jiki na ba. Gidajen rawa kawai na ke zuwa in zabi duk namijin da na ga ya yi min. Kanwar mahaifiya ta koya min yadda ake amfani da asiri domin janyo hankalin maza," in ji Stella.

Matar ta kara da cewa ba ta taba rashin sa'a ba ta hadu da maza wadanda ba su da kudi da za su biya ta yadda ta ke so. Ta kuma yi ikirarin cewa dukkan wadanda ta ke harka da su ba su taba zargin tana musu asiri ba kawai gani suke yi tana da fara'a da farin jini.

Stella ta kara bayani cewa tana da ikon samun duk wani na miji da ta ke so har ma ta saka ya tura mata kudi kimanin KSh 500,000 (N1,758,246.84) zuwa asusun ajiyar bankin ta. Da ta gama amfani da namiji, ta kan yi watsi da shi ne kuma ta masa asirin da zai sa ya dena jin yana sha'awar ta.

"Idan ina son namiji ya biya min kudin hayar gida na, kawai kiransa zan yi a waya in fada masa. Ina da asirin juya attajiran maza," in ji ta.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments