--
WAEC: Ganduje ya yi afuwa ga daliban kwaleji da suka yi mishi zanga-zanga

WAEC: Ganduje ya yi afuwa ga daliban kwaleji da suka yi mishi zanga-zanga

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya bada umarnin gafara ga dukkan daliban da suka shiga zanga-zangar da aka yi a kwalejin kimiyya na Dawakin Tofa da ke jihar Kano 

Ganduje ya yi masu afuwan ne domin yan aji shida su samu damar zana jarrabawar WAEC

Gwamnan ya kara da jan kunnen daliban da su kasance masu bin doka don tabbatar da cewa irin wannan lamarin bai sake faruwa ba a makarantar duk rintsi Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bada umarnin gafara ga dukkan daliban da suka shiga zanga-zangar da aka yi a kwalejin kimiyya na Dawakin Tofa da ke jihar Kano. 

A wata takardar da Lauratu Ado Diso, babbar sakatariyar ma'aikatar ilimi ta jihar Kano ta sa hannu a ranar Alhamis, ta ce Gwamnan ya bai wa ma'aikatar ilimi ta jihar umarnin. Ya ce a dawo da daliban aji shida na makarantar domin su rubuta jarabawar kammala sakandire, jaridar Sun ta ruwaito.

Wannan takardar ta fita ne dauke da kwanan wata 12 ga watan Augustan 2020, bayan an mika takardar ga kwamishinan ilimi na jihar, Muhammadu Sanusi S. Kiru, kafin a fara taron majalisar zartarwa ta jihar. A takardar, 

gwamnan ya kara da jan kunnen daliban da su kasance masu bin doka don tabbatar da cewa irin wannan lamarin bai sake faruwa ba a makarantar duk rintsi. An shawarci iyayen da suka biya wa yaran kudin jarabawar a makarantar da su gaggauta dawo da yaran kwalejin don fara shirin jarabawar, wacce za a fada a ranar 17 ga watan Augustan 2020. 

Wani mahaifi na daya daga cikin daliban, wanda ya bukaci a boye sunansa, ya nuna farin cikinsa yayin da ya tabbatar da cewa 'ya'yansu sun koyi darasi daga kuskurensu. 

A gefe guda, hukumar shirya jarrabawar makarantun sakadandare ta Najeriya, NECO, ta fitar da jadawalin jarrabawar shekarar 2020 da ka'idojin rubuta jarrabawar ta bana. Hakan na zuwa ne a lokacin da hukumar jarrabawar ta bayyana cewa za ta saka naurar daukan bidiyon sirri na CCTV a dakunan rubuta jarrabawar domin hana magudi.

Source: Legit.ng 

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "WAEC: Ganduje ya yi afuwa ga daliban kwaleji da suka yi mishi zanga-zanga "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?