--
Kada ku biyo dabi'armu, mun yi son kai, mun ji kunya - Ortom ga matasan Najeriya

Kada ku biyo dabi'armu, mun yi son kai, mun ji kunya - Ortom ga matasan Najeriya

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, a ranar Laraba ya ce shugabannin kasar nan sun ji kunya kuma sun kunyata Najeriya. Ya zama wajibi su fara neman gafara daga Allah. Ya bayyana hakan ne a taron murnar zagayowar ranar Matasa ta duniya da aka yi a Makurdi, 

babbar birnin jihar. Gwamnan ya bayyana yaki da rashawa da gwamnatin tarayya ke yi a matsayin zabe da son ganin bayan wasu. "Bari in fadi a nan cewa shugabannin kasar nan sun ji kunya, har da ni." Ortom ya bayyanawa matasa "Babban abin kunya ne ga mu shugabanni, wajibi ne mu nemi gafara daga Allah. Kuma ina baku shawara kada ku biyo dabi'armu. San kai babban kalubale ne." 

"Abubuwan da mukeyi basu dace ba, Akwai babban kalubale. Akwai wadanda doka bata aiki a kansu. akwai shanayen da baka isa ka taba ba, ko da sunyi abubuwa mara kyau, ba a isa a taba su ba." 

"Mutane na sace biliyoyi kuma ana kallonsu babu yadda aka iya da su amma ana daure wadanda sukayi satan kaza." 

Duk da haka Gwamnan ya ce idan Ubangiji ya bashi dama, yana son kwashe shekaru 90 kacal ne a duniya. Gwamnan zai cika shekaru 60 a duniya a 2021, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Kada ku biyo dabi'armu, mun yi son kai, mun ji kunya - Ortom ga matasan Najeriya "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?