LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Sakamakon binciken mu a kan hadimin Ganduje, Ali Baba - Rimin Gado

 

Hukumar sauraron korafi da yaki da rashawa ta jihar Kano, ta ce ta fadada bincike a kan mai bada shawara na musamman ga gwamnan jihar Kano a kan harkokin addini, Ali Baba Fagge kuma za a gurfanar da shi a kan zargin rashawa da ake masa. 

Shugaban hukumar, Muhyi Magaji ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Laraba a Kano a kan wannan ci gaban. Idan za mu tuna, an gayyaci Ali Baba Fagge tare da yaransa bayan korafin zargi sa da ake da dage kudin malamai na jihar da aka bada don yin addu'a ta musamman a kan korona. 


An zargi cewa yaransa ne suka rarraba from din da aka ware wa malaman. Muhyi Magaji ya ce hukumar ba an kafa ta bane don gurfanarwa, an kafa ta ne don tabbatar da cewa an yi komai yadda ya dace. Solacbase ta ruwaito cewa shugaban hukumar na yin martani ne a kan dalilin da yasa basu gurfanar da hadimin gwamnan ba.

"Abun takaici ne yadda aka kasa fahimta ta saboda hukumar ta yi bincike masu tarin yawa kuma ta samo dukiyoyin ba tare da ta gurfanar ba," Muhyi yace. 

"Toh a takaice ina cewa bayan bincikar Ali Baba Fagge, kuma aka kama shi da laifi, za mu tabbatar da mun kai shi gaban kotu." Kamar yadda Magaji yace, mutum bakwai cikin 10 na wadanda Fagge ya bai wa kudi, 

sun yi korafin rage wasu kudi daga N50,000 da aka ba su, wanda hukumar ta fara bincika. Ya ce, "A yayin binciken, mun gano cewa ba kamar yadda jama'a ke cewa ba a kan Fagge ya kwashe miliyoyin Naira bane. 

"Binciken ya nuna cewa wanda ake zargin an ba shi N50,000 don bai wa mutum 10 amma sai aka tursasa wasu su dawo da wani sashi na kudin. "Ina son tabbatar muku da cewa mun samo N310,000 kuma mun mayar wa mutanen da abun ya shafa kudin. "Amma mun fadada bincike mu a kan lamarin don gano sauran wadanda abun ya shafa."


 Source: Legit.ng 

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

 Post a comment

0 Comments