--
Kokunsan Garin da aka haramta latsa waya yayin tafiya?

Kokunsan Garin da aka haramta latsa waya yayin tafiya?

A duk lokacin da matafiya suka sauka daga jirgin ƙasa a garin Yamato, abin da za su fara cin karo da shi a tashar jirgin shi ne wata alama da ke nuna haramcin amfani da waya yayin da ake tafiya a ƙafa a kan titi.


Garin Yamato na da nisan kilomita 30 daga Tokyo babban birnin ƙasar Japan.


Wannan dokar da aka saka, jami'an ƙasar ne suka ƙirƙire ta - duk da ba a ɗaukar mataki mai tsanani ga waɗanda suka karya dokar.


Tilasta wa mutane daina latsa wayoyinsu yayin tafiya kan titi abu ne da ƙasashe da dama suke ke son a tabbatar.


Me ya sa hukumomi a Yamoto ke ganin wannan dokar da aka saka za ta iya sauya ɗabi'un mutanen garin?

'Akwai hatsari'

Tituna a Japan na cike da mutane da ake kira "arukisumātofon ", wanda hakan ke nufin masu tafiya suna latsa wayoyinsu. Wannan wata kalma ce inda aruki ke nufin (tafiya) sai kuma sumātofon na nufin (wayar zamani).


A watan Janairu, garin Yamato ya gudanar da bincike a wurare biyu inda aka gano cewa kashi 12 cikin 100 na mutum 6,000 da aka yi bincike a kansu suna latsa wayoyinsu yayin da suke tafiya kan tituna.


Magajin garin Satoru Ohki - wanda yana daga cikin wadanda suka shige gaba domin yin wannan doka - ya bayyana cewa hakan abu ne mai hatsari.

Tun da farko dai Mista Ohki ya bayar da shawarar yin wannan doka ga 'yan majalisa, bayan ya gama tuntuɓa sai ya gano cewa mutum takwas cikin 10 sun goyi bayan shawarar da ya kawo.


Bayan hakane a watan Yuni aka ƙaddamar da dokar hana latsa waya yayin da ake tafiya kan titi.


A kwanakin farko da aka fara amfani da wannan doka, garin na Yamato ya ɗauki ma'aikata da suke riƙe wasu alamu a hannunsu a daidai tashar jirgin ƙasar garin, alamun na ɗauke da bayanai da aka naɗa a faifan CD da ke bayani kan dokar.

Mista Ohki ya ce ba ya son ɗaukar ƙarin ma'aikata da za su rinƙa sintiri kan tituna domin tabbatar da an aiwatar da dokar sakamakon annobar korona, a halin yanzu dai alamomin da aka saka a hanyar fita daga tashar jirgin ƙasan ne kaɗai alamun wannan dokar. "Na yi ammanar cewa mutanen Yamato za su bi doka," in ji shi.


Wata mai suna Atsuko Nabata, ta bayyana cewa a duk lokacin da take tuƙa keke, sai tana yi tana kauce wa masu latsa waya.


Ba wannan ne karo na farko ba da wata ƙasa ke ɗaukar irin waɗannan matakan ba domin guje wa hatsari.


Ilsan, wani gari ne a Koriya Ta Kudu, an taɓa saka wasu fitulu kan hanyar da masu tafiya a ƙafa ke tafiya da ke gargaɗinsu kan su daina latsa waya idan suna tafiya.


Amma a Yamato, har yanzu babu wani mataki da ake ɗauka ga waɗanda aka kama ko kuma samu da laifin suna latsa waya yayin da suke tafiya kan titi.


Mataki mai kyau

A bayyana take cewa mutanen Japan suna sane da wannan hatsarin na amfani da wayoyi yayin tafiya kan titi.


A 2019, wani bincike da aka gudanar kan mutum 562 da ke amfani da wayoyi a Japan ya nuna cewa kashi 96.6 cikin 100 sun bayyana cewa suna sane da hatsarin da ke cikin amfani da waya yayin tafiya, kashi 13.2 cikin 100 kuma sun bayyana cewa sun taɓa cin karo da juna yayin da suke tafiya suna latsa waya, kashi 9.5 cikin 100 kuma sun ce sun taɓa jin ciwo.


"Na amince da wannan doka," in ji Tokyo Atsuko Nabata, mai shekaru 60, kuma tana yawan tuƙa keke kan titunan Tokyo. "A duk lokacin da nake tuƙa keke, sai ina yi ina kauce wa masu latsa waya, an taɓa bige ni," in ji ta.


"Idan mutane masu amfani da wayoyinsu na tunkarata, dole sai na tsaya na bari sun wuce. A 'yan kwanakin nan idan na kusan karo da wani da ke latsa wayarsa, ba na tsayawa bayar da haƙuri, ina wucewa ne kawai, duk da cewa cikin raina ji nake yi kamar na yi ihu."


SOURCE: BBCHAUSA

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Kokunsan Garin da aka haramta latsa waya yayin tafiya?"

Post a Comment

Tell us what you think about this article?