LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

A Jihar Borno Ma An Kubutar Da Wani Yaro Da Aka Killace Shi Na Tsawon Lokaci, Inda Ake Ba Shi Abinci Sau Daya A Rana

An kubutar da wani yaro dan shekaru sha uku da haifuwa mai suna Aminu wanda aka ajiye shi a baranda a nan yake kwana komai zafi ko sanyi. Kuma sau daya suke ba shi abinci a yini, kamar yadda baban yaro ya shaidawa wadanda suka kubutar shi.
Aminu dai da mahaifin sa Malam Murtala  da matansa suna zaune a titin Baga dake cikin Maiduguri.
Tun bayan sakin mahaifiyar Aminu da mahaifinsa ya yi aka ajiye shi a baranda na tsawon lokaci.

Kungiyar (National human rights commission) karkashin jagorancin Barista Jummai Mishelia ne suka kubutar da Aminu, inda yanzu Malam Murtala da matan sa suke hanun hukuma, yayin da shi kuma Aminu yake karkashin kulawar wadanda suka kubutar da shi, inda za su kai shi asibiti domin duba lafiyar sa
Hotuna: Junaid Jibril Maiva
Daga Real Sani Twoeffect Yawuri
Source: Shafin Rariya Na Facebook
DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments