--
Yan sanda sun ceto mutumin da aka rufe shi a gida tsawon shekaru 15 a Sokoto ba fita

Yan sanda sun ceto mutumin da aka rufe shi a gida tsawon shekaru 15 a Sokoto ba fita

 Ƴan sanda jihar Sokoto sun ceto wani mutum mai shekaru 45, Salisu Muhammad da kawunsa ya ɗaure shi a gida na tsawon shekaru 15 a Gidan Madi a ƙaramar hukumar Tangaza. 


An ce Muhammad wadda ke da yarinya da ta girma yana fama da taɓin hankali ne kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. 


Hajiya Ubaida Bello, mai bawa Gwamna Aminu Tambuwal shawara a kan Hakokin Bil Adama da Kungiyoyin tallafawa al'umma ce makwabta ne suka sanar da hukuma game da halin da ya ke ciki don da farko sunyi tsammanin ya mutu ne. 


"Da farko sunyi tsammanin ya mutu ne domin ba su gan shi ba a waje na tsawon shekaru fiye da goma. "Da suka gano halin da ya ke ciki, sun sanar da mu cikin gaggawa. 


"Daga nan ne muka tattara ƴan sanda, masu kare hakkin bil adama da wasu ma'aikatan ƙaramar hukuma ciki har da shugaban ƙaramar hukuma muka tafi gidan muka ceto shi," in ji ta. 


An gano wasu mata biyu a gidan ciki har da ƴarsa mai shekaru 19 wadda a yanzu ba ta san tsawon lokacin da ya yi a daure ba. 


"Mun tarar da shi a cikin mummunan yanayi, yana bayan gida da fitsari a wuri guda ba tare da wani kulawa ba. "Ya kasa yin tafiya da kansa ma saboda rashin samun abinci.


 "Idan suna iƙirarin cewa yana fama da taɓin hankali ne me yasa ba su kai shi asibitin ƙwaƙwalwa ba domin ayi masa magani," in ji ta. 


Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa kawun mutumin ne da ke zaune a wani ƙauye nan kusa ya rufe shi.


 Bello ta ce an garzaya da mutum asibitin ƙwaƙwalwa a karamar hukumar Ƙware yayin da ƴan sanda na cigaba da bincike don gano dalilin rufe shi. 


Kakakin ƴan sandan jihar Sokoto ASP Muhammad Sadiq ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce binciken da suka fara yi ya nuna mutumin na da taɓin hankali. "Kawo yanzu babu wanda aka kama a kan lamarin," in ji shi. 


SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG

LATSANAN DOMIN SAMUN LABARAI TA WHATSAPP:
https://chat.whatsapp.com/KKAd5L0NolZ4F6yJqdblUO

SAYI  KWAKWKWARAR  DATAR MTN  MAI KYAU DA INGANCI ANAN DOMIN SIYA YANZU LATSA NAN↓↓↓
https://paystack.com/pay/mz-st-fdub

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: 
https://www.bzglobalservice.com.ng/

KU BIYOMU A SHAFUKAN

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Bzglobalservice.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/bzglobalsevice

KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

0 Response to "Yan sanda sun ceto mutumin da aka rufe shi a gida tsawon shekaru 15 a Sokoto ba fita "

Post a Comment

Tell us what you think about this article?