LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Kasashe 10 da su ka fi tara manyan masu kudi a Duniya a shekarar 2020

Kusan rabin attajirai 2100 da ake da su a Duniya su na zama ne tsakanin Amurka da kasar Sin. Asali ma a shekarar nan ta 2020, adadin Attajirai a sauran kasashe ya na raguwa ne. Mujallar Forbes da CEO World sun ce Attajiran da ake ji da su a Duniya sun ragu daga 2, 153 zuwa 2, 095 a bana.

Amurka mai mutum 614, ta fi kowace kasa yawan masu kudi a yau. Mai kamfanin Amazon, Jeff Bezos shi ne wanda ya kerewa kowane mai kudi a ban kasa. Duk da cewa Attajirain Amurka su na yin kasa, arzikin Bezos karuwa ya ke kara yi a halin yanzu.

Kasar Sin ce ta zo ta biyu a wannan jeri da Attajirai kusan 390. Manyan kasashen biyu su na da Attajirai kimanin 10000 wanda kowane dukiyarsa ta haura akalla Dala biliyan guda. Wannan lisafi da aka yi ba ya kunshe da jerin Attajiran kasar Hong Kong da Macao. Idan an hada jimillar Attajiran Sin da na wadannan kasashe, za a samu mutane fiye da 450.

Sauran kasashen da su ka biyo bayan Amurka da Sin sun hada da Jamus, Indiya, Brazil da kuma Faransa. Mujallar Forbes ta ce a wadannan kasashe, masu kudi sun rage yawa a 2020. Idan aka yi lissafin ta fuskar Nahiya, bangaren Asiya ta na da mutane 778 wanda su ka mallaki fam Dala tiriliyan 2.5 na kaf arzikin Duniya. Akwai Attajirai 120 a yankin Kanada da Latin.

Attajiran da Duniya ta ke ji da su 72 kadai su ke cikin Nahiyar Afrika da gabas ta tsakiya. A shekarar da ta gabata, an samu masu kudin a-zo-a-gani 85 a kasashen wannan yanki. Najeriya ta na da mutane hudu a cikin wadannan fitattun Attajirai.

Na farkonsu shi ne Aliko Dangote. Sauran sun hada da Mike Adenuga, Abdussamad Rabiu da Folurinsho Alakija. Ga yadda alkaluman su ke: 1. Amurka: 614 2. Sin: 389 3. Jamus: 146 4. Indiya: 102 5. Rasha: 99 6. Hong Kong: 66 7. Brazil 45 8. Ingila 45 9. Kanada 44 10. Faransa 30 SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments