LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

An Kubutar da Wani Mutum Da Yaso Kashe Kansa Saboda Bashin N500,000

Mahaifin yara biyu, Adeyinka Abiodun, an kubutar dashi daga kashe kansa kan bashin N500,000.

Abiodun wanda ke zaune a yankin Ikotun na jihar Legas yayi kudurin kashe kansa ta hanyar tsalla zuwa cikin wani rafin dake a jihar.

Burin na shi bai cika ba yayin da jami’an ‘yan sanda da ke aikin suka kame shi cikin hanzari.
Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda a Legas, Bala Elkana, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa ranar Lahadi.


Ya bayyana cewa jami’an tsaron sun dakile yunkurin kisan kai da misalin karfe 1:50 na daren Juma’a a makon da ya gabata yayin da aka kubutar da wanda yai niya kashe kanshin kuma aka kai shi ofishin ‘yan sanda da ke Bariga don yin tambayoyi da kuma bayar da bayanai.


A cewar Elkana, Abiodun ya ba da labarin cewa ya samo rancen N390,000 a watan Maris tare da shirin biyan wata-wata na watanni shida da karbar ribar N142,287 daga bankin microfinance a jihar Legas.


An ce ya karba rancen ne da niyyar inganta kasuwancinsa na sayar da giya, amma kasuwancin ya gaza kuma an yi asarar kudin.
Lokacin da ‘yan sanda suka tuntube shi, bankin microfinance ya tabbatar da cewa mutumin ya karba bashin.

SOURCE:HUTUDOLE.COM

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN

KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments