LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Karin 'yan Najeriya 443 sun kamu da korona, jimilla 45,687

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Najeriya wato NCDC ta bayyana cewa annobar cutar Covid-19 ta sake harbin sabbin mutane 443 a fadin Najeriya. Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da hukumar NCDC ta fitar da misalin karfe 11:26 na daren ranar Juma'a 7 ga Agustan shekarar 2020.

A cikin sanarwar da NCDC ta saba fitarwa a daren kowacce rana a shafinta na Twitter, ta sanar da cewa an samu karin sabbin mutane 443 da suka fito daga jihohin Najeriya kamar haka:

Plateau-103

Lagos-70

FCT-60

Ondo-35

Edo-27

Rivers-27

Kaduna-20

Osun-19

Borno-18

Oyo-18

Kwara-11

Adamawa-9

Nasarawa-7

Gombe-6

Bayelsa-4

Imo-4

Bauchi-2

Ogun-2

Kano-1 Alkalluman da hukumar ta dakile cututtukan ta fitar a ranar Juma'a 7 ga watan Agusta shekarar 2020 ya nuna cewa jimillar wadanda suka kamu da cutar ta korona a kasar 45,687.

An sallami mutum 32,637 bayan an tabbatar da sun warke sarai, a yayin da cutar ta hallaka jimillar mutane 936.


SOURCE: LEGITT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments