LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Champions League: An yi waje da Real Madrid da kuma Juventus

Manchester City ta kammala aikin da ta soma a cikin watan Fabarairu inda ta doke Real Madrid a gasar zakarun Turai.

City ta casa Real da ci biyu da daya a wasan da suka buga a Etihad, inda Sterling da Jesus suka ci kwallo sai kuma Benzema ya farkewa Real kwallo daya.

'Yan wasan Pep Guardiola za su hadu da Lyon a zagayen gabda na kusa da karshe.

Wannan rashin nasarar it ace ta farko da Zinedine Zidane a zagaye na biyu a matsayin koci a gasar zakarun Turai.

Juventus da Lyon

A daya wasan da aka buga a ranar Juma'a da daddare, kungiyar Lyon ta fitar da Juventus daga cikin gasar duk da cewa Ronaldo ya zuwa kwallo biyu a wasansu.

A ranar Asabar, Barcelona za ta dauki bakunci Napoli sai kuma karawa tsakanin Bayern Munich da Chelsea.

Duk da cewa ta lashen gasar La Liga amma wasannin karshe na gasar sun nuna a irin yadda Madrid ba ta iya zira kwallaye ma su yawa kamar a baya.

Mafi yawan 'yan wasan Madrid sun fara gajiya saboda yawan buga wasanni kamar su Benzema da Modric da Kroos da dai sauransu.

Sai dai Bale wanda ke da alaka mai tsami tsakaninsa da mai horas da kungiyar Zinedine Zidane watakila ba zai buga wasan ba.

Amma ana yiwa Zinedine Zidane kallon mai nasara a wannan gasa don haka wasu na ganin ba za a iya hasashen mai zai faru ba har sai an buga wasan.

SOURCE: BBCHAUSA

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUNKU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657


Post a comment

0 Comments