LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Gawurtaccen ɗan daba ya shiga hannun 'yan sanda a Kano

Wani fitaccen dan daba da ya gawurta mai suna Aminu A. Aminu, ya shiga hannun jami'an tsaro na 'yan sanda a birnin Kanon Dabo. Kafar watsa labarai ta Gidan Rediyon Freedom ta ruwaito cewa, Aminu mai shekaru 21 a duniya ya fada tarkon jami'an tsaro bayan ya aikata mummunar ta'asa a baya bayan nan.

An ruwaito cewa, Aminu ya kasance fittacen dan sara suka da ya addabi al'ummar Unguwanni Kwalli da Sagagi da ke karkashin karamar Hukumar birni a Kano. Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ne ya sanar da hakan yayin zantawa da manema labarai.

DSP Kiyawa ya ce mutumin da ake zargi ya shiga hannu ne bayan sun samu korafi daga wani matashi mai shekaru 31 mazaunin unguwar Sagagi, Mubarak Abdul, wanda ya shigar da karar cewa Aminu ya kafta masa sara da wuka a wuya.

Kamar yadda babban jami'in dan sandan ya bayyana, nan da nan a ka garzaya da shi asibitin Murtala yayin da ake ci gaba da bincike domin gurfanar da wanda ake zargi a gaban Kuliya.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUN


KU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments