LABARAN YANZU

6/Labari/ticker-posts

Kotu ta raba wasu ma'aurata saboda matar ba ta yarda mijin ya kusanci shimfidar ta

Wata kotun gargajiya da ke zamanta a Mapo a garin Ibadan a ranar Juma'a ta datse igiyar auren Abidemi Dada, Injiniya, da Opeyemi saboda ƙauracewa shimfidarsa da rashin mutunta shi.

Yayin yanke hukuncin, Shugaban kotun, Cif Ademola Odunade, ya ce babu shakka ƙaunar da ke tsakanin Dada da Opeyemi ya gushe.

Ya raba ƴaƴansu hudu tsakaninsu. Wanda yayi karar an bashi ƴaƴa biyu na farko, wacce aka yi ƙarar ta kuma aka bata sauran biyun.

"Wannan kotun ta yi iya ƙoƙarin ta domin ganin an sulhunta ma'auratan amma dukkansu sunƙi canja matsayansu.

"Ina bawa ma'aurata da ma waɗanda ba suyi aure ba shawara su dena saurin fushi," in ji shugaban kotun.

Abidemi da ke zaune a Oke-Ado, a ranar 19 ga watan Maris ya yi karar matarsa inda ya ce tana hana shi haƙƙin kwanciyar aure kuma bata girmama shi.

"Ta ƙi amfani da shawarar da kotu ta bamu da farko na sauya halayen ta. Ba ta sauke nauyin da ya rataya a kanta a matsayin ta na matar aure. "Lamarin ya cigaba da tabarbarewa har ta kai ga ta dena kwanciya a daki na kuma ta dena kula da yaran mu.

"Ta koka cewa bata da lafiya, na kai ta Asibitin Koyarwa ta Jami'a, UCH, aka bata magani kuma likita ya ce ta warke. "Opeyemi ta taɓa faɗa min cewa ji ta ke kamar ta daɓa min wuƙa ta kashe ni. Ba na son in mutu kafin lokaci na,"

in ji Abidemi. Opeyemi wacce ke zaune a Oke-bola a Ibadan ta amince da raba auren kuma ba ta musanta zargin da aka yi mata ba.

Ta amsa cewa a sane ta aikata duk abinda ta yi kuma ta yi hakan ne domin ta samu kwanciyar hankali.

SOURCE: LEGIT.NG

DAGA: BZGLOBALSERVICE.COM.NG


KU AIKO MANA DA LABARI KO SHAWARWARI KO MAGANA DAMU KAITSAYE TA ADRESHIN EMAIL: bzglobalservicelabari@gmail.com

KARANTA WASU SABBIN LABARAI ANAN: https://www.bzglobalservice.com.ng/
LATSANAN DOMIN SAMUNKU SAUKE MANHAJARMU TA ANDROID APPLICATION AWAYOYINKU NA HANNU KYAUTA DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI: https://www.appcreator24.com/app757657

Post a comment

0 Comments